Home Back

Gwamnan Zamfara Ya Rabawa Makarantu 250 Kayan Karatu Da Fitilu Masu Amfani Da Hasken Rana A Jihar

leadership.ng 2024/4/28
Gwamnan Zamfara Ya Rabawa Makarantu 250 Kayan Karatu Da Fitilu Masu Amfani Da Hasken Rana A Jihar

A wani biki da aka gudanar a yau Laraba a Gusau, babban birnin Jihar Zamfara, gwamna Dauda Lawal ya kaddamar da rabon kayayyakin karatu a makarantun firamare 250 a fadin jihar.

Tallafin kayan karatun, hadin gwiwa ne tsakanin hukumar Ilimin bai daya ta Jihar (ZUBEB) da ta kasa (UBE) da kuma hukumar kula da Karatun kananan yara ta majalisar dinkin Duniya (UNICEF).

A jawabinsa, gwamna Dauda Lawal ya bayyana cewa, kayayyakin da za a raba na makarantu 250 ne, wadanda suka kunshi Littattafan Karatu 242,176 na fani daban-daban, ECCDE 200, ECCDE kujeru da tebura 25, kayan gwaje-gwaje 8,210 da Fitilu masu amfani da hasken rana daga UNICEF (NLP) don samar da haske a makarantun.

A yayin bikin kaddamar da kayayyakin, Gwamna Lawal ya bayyana cewa, jihar Zamfara da ke fama da karancin ilimi a Nijeriya, za ta ci gaba da bada tallafi da hadin kai ga abokan huldar kasa da kasa domin ciyar da ilimi gaba a jihar.

Ya ce, “Na yi farin cikin kasancewa a wannan gagarumin taron na raba kayan karatu ga dalibai a wannan sashin namu na ilimi. Wannan karamcin na daya daga cikin dimbin ayyukan da jihar Zamfara ke amfana da su.

“Muna aikin gyaran makarantun Sakandare 60 a fadin jihar nan karkashin hukumar taimakon al’umma da ci gaban al’umma ta bankin duniya (CSDA). Kowace karamar hukuma tana da makarantun sakandare shida (6) da ake gyarawa, yayin da babban birnin jihar Gusau ke da takwas (8).

“Dokar ta-baci na ilimi da aka ayyana a jihar, bata ta’allaka ga ilimin farko da sakandare kawai ba har da manyan makarantu. Mun sanya dokar ta-baci a manyan makarantun jihar.”

Bugu da kari, gwamnan ya bayyana matakan da gwamnatinsa ta dauka na sasanta basussukan WAEC da NECO da gwamnatocin baya na jihar suka gaza biya.

Gwamna Dauda ya Kuma tabbatar da cewa, duk Shugaban Makarantar da aka samu wajan karkatar da kayan da aka raba ko aka sace Fitilun, to, a bakin aikin shugaban.

 
People are also reading