Home Back

‘Yancin Kananan Hukumomi: Majalisa Na Shirin Hana Bai Wa Gwamnoni 21 Kason Kudinsu Na Tarayya

leadership.ng 2024/8/25
majalisar kasa

Majalisar wakilai na shirin hana bai wa gwamnoni 21 kason kudinsu na tarayya bisa rashin gudanar da zaben kananan hukumomi a jihohinsu.

An zartar da wannan hukunci ne biyo bayan amincewa da kudirin gaggawa na magance kin bin ka’idojin dimokuradiyya da gwamnatocin jihohi suke yi na tauye hakkin kananan hukumomi wajen kin gudanar da zaben kananan hukumomin tare da nada kantomomin riko, wanda dan majalisar wakilai Hon. Ademorin Kuye ya gabatar.

Don haka, majalisar ta umarci kwamitocin hadin gwiwa kan harkokin kudi, tattara kudaden shiga da rabon kudaden tarayya (RMAFC) da su hana kason kananan hukumomi na jihohin da ba su yi zaben kananan hukumomi ta hanyar dimokuradiyya ba.

Majalisar wakilai ta umurci RMFAC da ta kirkiro wani asusu na musamman wanda za a rika biyan irin wadannan kudade har sai an gudanar da zaben kananan hukumomi ta hanyar dimokuradiyya a wadannan jihohi guda 21.

‘Yan majalisar sun kuma umarci ofishin babban mai shari’a na kasa (oAuGF) da ya kaddamar da shari’a a kan duk jihar da ta dakatar da wa’adin shugabannin kananan hukumomin da bai kare ba tare da umurtar RMFAC da ta hana kudaden kasafi na tarayya ga wadannan gwamnatocin jihohi.

Don haka majalisar ta umarci kwamitinta na kula da bin doka ya tabbatar an bin wannan ka’ida.

People are also reading