Home Back

Tinubu Ya Tura Sako ga Shugabannin Arewa, Tare da Barazanar Korar Masu Mukamai

legit.ng 2024/6/26
  • Shugaban kasa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya gana da tawagar kungiyar dattawan Arewa (ACF) a fadar shugaban kasa
  • Bola Tinubu ya ba su umurnin komawa gida su hada kai wajen duba matsalolin Arewa tare da kuma gaggauta nemo mafita
  • Shugaban ya kuma bayyana mataki mai tsauri da gwamnatin sa za ta dauka kan dukkan jami'an sa da suka yi kasa a gwiwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Arewa - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya gana da kungiyar dattawan Arewa (ACF) a ranar Alhamis.

Bola Tinubu ya koka kan yadda tarin matsaloli suka addabi yankin Arewa ba tare da an nemo mafita ba.

Tinubu
Tinubu ya bukaci 'yan Arewa da su magance matsalolin yankin. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu. Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa shugaban kasar ya umurce su da su koma gida su hada kai da jami'an gwamnati domin samar da mafita ga yankin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sakon Bola Tinubu ga manyan Arewa

Shugaba Bola Tinubu ya yi kira da samar da haɗaka tsakanin gwamnonin Arewa da sauran jami'an gwamnati domin magance matsalolin yankin.

Tinubu ya ce akwai matsalolin yaran da ba su zuwa makaranta, talauci da rushewar tattalin arziki da ya kamata shugabannin Arewa su magance da gaggawa.

Tinubu: "Kar ku manta da ƙauyuka"

Cikin sakon da shugaban kasar ya isar, ya ce kada idan an tashi magance matsalolin ana mantawa da mutanen karkara, rahoton Vanguard.

Ya ce mutane da dama suna karkara suna ayyukan noma da sauransu kuma ƙananan hukumomi ba su da karfin da za su tallafa musu. Saboda haka ya ce kar su manta da su.

Shugaba Tinubu zai kori masu mukamai

Shugaban kasar ya ce a halin yanzu gwamnonin jihohi suna samun kuɗi sosai daga gwamnatin tarayya saboda haka kowa ya koma gida domin magance matsalolin yankinsa.

Ya tabbatar da cewa duk wanda ya gaza a cikin jami'an gwamnatinsa to lallai zai sallame shi daga aiki.

An soki Tinubu kan tsadar tumatur

A wani rahoton, kun ji cewa manoma tumatur a Najeriya sun koka kan yadda tsare-tsaren gwamnatin shugaba Bola Tinubu suka kawo tsadar kayan gwari.

Shugaban kungiyar masu nomar rani a jihar Bauchi ya ce cire tallafi man fetur da karin kudin wutar lantarki sun hana manoma da dama nomar rani a wannar shekarar.

Asali: Legit.ng

People are also reading