Home Back

ƘARANCIN KUƊI: Hukumar Alhazai ta rage ƙuɗin da take baiwa ma’aikatan wucin gadin da na hukumar da ke aikin Hajji bana

premiumtimesng.com 2024/7/3
ƘARANCIN KUƊI: Hukumar Alhazai ta rage ƙuɗin da take baiwa ma’aikatan wucin gadin da na hukumar da ke aikin Hajji bana

Shugaban Hukumar Alhazai na Kasa Jalal Arabi ya koka da ƙarancin kuɗi da hukumar ke fama shi da ya sa dole ta dakatar da wasu alawus da take ba ma’aikatan ta na wucin gaɗi da ke aiki a kasa mai tsarki.

Arabi, ya bayyana haka ne a wata sanarwa da mataimakiyar daraktar hulda da jama’a ta hukumar, Fatima Sanda-Usara, ta fitar ranar Alhamis a Abuja.

Arabi ya bayyana cewa tabarbarewar harkokin kuɗi da ta shafi bangarori da dama na ayyukan hajjin 2024 bai bar biyan ma’aikatan NAHCON albashi da alawus na aikin hajjin ba.

Saboda wadannan matsalolin kudi, wasu alawus-alawus na musamman ga ma’aikatan NAHCON za su ci gaba da kasancewa an dakatar da su.

Duk da wannan yanayi na kalubale, hukumar na ci gaba da fatan cewa yayin da yanayi ya inganta, za a duba lamarin sannan a ɗan yi musu ƙari a alawus ɗin.

Sai dai a wannan karon, za a baiwa ma’aikatan zabin komawa Najeriya bayan sun shafe kwanaki 21 suna aiki idan sun zabi komawa. ”

A ƙarshe ya godewa ma’aikatan bisa goyon baya da fahimta da suka ka yi game da matsalolin da hukumar ke ciki da tsananin rashin kuɗi.

People are also reading