'Yan Sanda Sun Ragargaji 'Yan Bindiga a Wani Samame a Jihar Benue
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Benue - Jami'an rundunar ƴan sandan jihar Benue sun yi nasarar hallaka ƴan bindiga mutum biyu.
Ƴan sandan sun samu nasarar ne bayan da suka kai hari a sansanin ƴan bindigan da ke a gundumar Mbatyula cikin ƙaramar hukumar Katsina-Ala a jihar.
Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar, Catherine Anene, ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa, cewar rahoton jaridar Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Catherine ta ce an samu nasarar ne sakamakon ci gaba da ƙoƙarin da ƴan sanda ke yi na murƙushe ƴan bindiga a yankin Sankera na jihar cikin watanni uku da suka gabata, rahoton New Telegraph ya tabbatar.
"Jami'an ƴan sanda na Operation Zenda JTF sun farmaki maɓoyar ƴan bindiga a ƙauyen Tse Uza, da ke gundumar Mbatyula a ƙaramar hukumar Katsina-Ala a ranar Lahadi, 30 ga watan Yunin 2024."
"Bayan sun isa sansanin, ƴan bindiga sun buɗe musu domin hana su shiga amma ƴan sandan sun ci ƙarfinsu."
"Likita ya tabbatar da mutuwar biyu daga cikin ƴan bindigan da suka samu raunuka, sannan an ajiye gawarwakinsu a babban asibitin Ukum yayin da sauran waɗanda ake zargi suka tsere."
- Catherine Anene
Catherene Anene ta ce kayayyakin da aka ƙwato daga sansanin sun haɗa da ƙananan bindigu guda biyu cike da harsasai, bindigu ƙirar gida guda uku, babura guda 13, mota ƙirar Toyota Corolla guda ɗaya da keke mai ƙafa uku guda ɗaya
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu ƴan bindiga da ba a san ko su waye ba sun kai farmaki kan jami'an tsaro a shingen binciken ababen hawa a jihar Abia.
Ƴan bindigan sun buɗe wuta tare da halaka jami'an ƴan sanda biyu a harin da suka shingen bincike da ke garin Aba a jihar da ke Kudu maso Gabashin Najeriya.
Asali: Legit.ng