Home Back

Maniyyata Hajji Biyu Daga Kwara Sun Mutu

leadership.ng 2024/7/5
Maniyyata Hajji Biyu Daga Kwara Sun Mutu

Wasu maniyyata biyu daga jihar Kwara Salihu Mohammed da Hawawu Mohammed sun rasu a birnin Madina a Saudiyya.

Salihu Mohammed ya rasu ne a sashen kula da marasa lafiya na asibitin gwamnati bayan ya yi fama da rashin lafiya.

A wani lamari mai ban tausayi, Hawawu Mohammed ta daka tsalle daga saman rufin masaukinta, kamar yadda hukumomin Saudiyya suka tabbatar ta faɗo ƙasa.

Hukumar Alhazai ta jihar Kwara ta jajantawa iyalan waɗanda suka rasu a wata sanarwa da ta fitar a yau Lahadi.

Sakataren zartarwa AbdulSalam AbdulKabir ya yi matuƙar kaduwa a hukumar game da rasuwar, inda ya yi ta’aziyya da kuma mika wuya ga hukuncin Allah a cikin dukkan al’amura.

Hukumar ta kuma yi addu’ar Allah ya jikan wadanda suka rasu ya kuma gafarta  musu.

People are also reading