Home Back

Sojojin Sama Sun Mayar da Martani, Sun Halaka Ƴan Bindiga da Yawa Bayan Harin Kankara

legit.ng 2024/7/1
  • Sojojin saman Najeriya sun mayar da martani, sun kashe tulin ƴan bindiga a jihar Katsina bayan harin da aka kai yankin Ƙankara
  • Sakataren watsa labaran gwamna, Ibrahim Kaula ya ce rahotanni bayan samamen sojin ya nuna ƴan bindiga 29 sun bakunci lahira
  • Ya ce wannan somin taɓi ne domin dakarun sojojin sama da na ƙasa za su ƙara haɗa kai da jami'an tattara bayanan sirri domin kakkaɓe ƴan ta'adda

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Katsina - Rundunar sojin saman Najeriya ta yi nasarar kashe ‘yan bindiga 29 a wani samame da ta kai a yankin karamar hukumar Bakori ta jihar Katsina.

Dakarun sojojin sun kaddamar da wannan luguden wuta ne biyo bayan harin da ƴan bindigar suka kai kauyen Gidan Guga a ƙaramar hukumar Ƙanƙara ranar Lahadi.

Sojojin Najeriya.
Sojoji sun kashe ƴan bindiga da yawa a yankin ƙaramar hukumar Bakori a jihar Katsina Hoto: Nigeria Army Asali: Twitter

A rahoton jaridar Leadership, wannan na ɗaya daga cikin matakan da jami'an tsaro suka ɗauka domin tabbatar da tsaro a yankunan da ƴan bindiga suka mamaye.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan nasara na ƙunshe ne a wata sanarwa da sakataren watsala labaran gwamnan Katsina, Ibrahim Kaula, ya fitar.

Kaula ya bayyana cewa harin da sojojin suka kai ta sama a kusa da tsaunin Bakori da Yartsintsiya da ke yankin Kankara ya sheƙe kimanin ‘yan bindiga 29.

"Rahotannin da muka samu bayan luguden wuta ta sama sun nuna cewa ƴan bindiga 8 sun baƙunci lahira sakamakon harbin bindiga yayin da ruwan bama-bamai ya sheƙe wasu 21.
"Duk da har yanzun ba a gama tattara bayanai ba, amma samamen ya ruguza harkokin ƴan ta'adda kuma mutane da dama da aka yi garkuwa da su sun kuɓuta.
"Daga cikin wadanda suka shaƙi iskar 'yanci har da diyar basaraken kauyen Ruwan Godiya, wacce ta shafe watanni da dama a hannun masu garkuwa."

- Ibrahim Kaula.

Ya ƙara da cewa sojojin sama da na ƙasa za su kara haɗa kai da hukumomin tattara bayanan sirri domin gano ƴan bindiga da murkushe su a yankin, cewar rahoton Guardian.

Gwamna Lawal ya koka kan halayen sojoji

A wani rahoton kuma Gwamnan Zamfara ya nuna damuwa kan yadda sojoji da ƴan sanda suka sa wasa a lamarin yaƙi da ƴan bindiga a Arewa maso Yamma.

Dauda Lawal ya ce halayyar jami'an tsaron waɗanda ke karkashin gwamnatin tarayya ne ya sa shi kafa rundunar asakarawan Zamfara.

Asali: Legit.ng

People are also reading