Muhimman Abubuwa 3 da Ya Dace a Sani a Kan Jami’in Kwastam da Ya Mutu a Majalisa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - A yau Litinin ne jami'in hukumar kwastam Etop Andrew Essien ya yanki jiki ya fadi yana tsaka da bayani a majalisar wakilai.
Hukumar kwastam ta tabbatar da rasuwarsa tare da tura sakon ta'aziyya ga ilayansa da Najeriya baki daya.
Legit tattaro muku abubuwa masu muhimmanci a kan Etop Andrew Essien kamar yadda hukumar kwastam ta wallafa a shafinta na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hukumar kwastam ta tabbatar da cewa Etop Andrew Essien ya shafe shekaru sama da talatin yana aiki tare da ita.
Etop Andrew ya shiga aikin kwastam ne a ranar 27 ga watan Nuwambar shekarar 1989 wanda lissafi ya nuna ya shafe shekaru 35 yana aiki.
Bincike ya tabbatar da cewa an haifi Etop Andrew Essien a ranar 16 da watan Nuwamba a shekarar 1967 a jihar Akwa Ibom.
Etop Andrew ya fito ne daga karamar hukumar Nsit-Ubium dake jihar Akwa Ibom a kudu maso kudun tarayyar Najeriya, rahoton Daily Trust.
Daga cikin manyan matsayin da Etop Andrew Essien ya rike a hukumar kwastam akwai mataimakin kwanturola a kan harkar tatttara haraji.
A kan wannan matsayin ne kuma Etop ya rigamu gidan gaskiya yayin da yake bayani a majalisar wakilai a yau Litinin, 25 ga watan Yuni.
A wani rahoton, kun ji cewa hukumar kwastam ta kasa ta yi alwashin kawo karshen matsalar boye abinci da ta addabi daukacin al'ummar Najeriya.
Kwastam ta ce a yanzu haka ta dauki masu matakai wanda za su kawo karshen matsalar domin kawo saukin rayuwa ga talakawan Najeriya.
Asali: Legit.ng