Home Back

Muhimman Abubuwa 3 da Ya Dace a Sani a Kan Jami’in Kwastam da Ya Mutu a Majalisa

legit.ng 2024/7/2
  • A yau Talata ne babban jami'in kwastam mai suna, Etop Andrew Essien ya fadi ya mutu yana cikin bayani a majalisar wakilai
  • Hukumar kwastam ta kasa ta fitar da sakon ta'aziyya inda ta ce Etop Andrew Essien jajircaccen jami'in ne da ya yi aiki tukuru
  • A wannan rahoton, Legit ta tatttaro muku abubuwa uku masu muhimmanci da ya kamata ku sani a kan Etop Andrew Essien

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - A yau Litinin ne jami'in hukumar kwastam Etop Andrew Essien ya yanki jiki ya fadi yana tsaka da bayani a majalisar wakilai.

Hukumar kwastam ta tabbatar da rasuwarsa tare da tura sakon ta'aziyya ga ilayansa da Najeriya baki daya.

Hukumar kwastam
Abubuwa masu muhimmanci kan jami'in kwastam da ya mutu a majalisa. Hoto: Uche Nnadozie Asali: Facebook

Legit tattaro muku abubuwa masu muhimmanci a kan Etop Andrew Essien kamar yadda hukumar kwastam ta wallafa a shafinta na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Etop ya shafe shekaru kusan 40 a aiki

Hukumar kwastam ta tabbatar da cewa Etop Andrew Essien ya shafe shekaru sama da talatin yana aiki tare da ita.

Etop Andrew ya shiga aikin kwastam ne a ranar 27 ga watan Nuwambar shekarar 1989 wanda lissafi ya nuna ya shafe shekaru 35 yana aiki.

Etop ya fito daga jihar Akwa Ibom

Bincike ya tabbatar da cewa an haifi Etop Andrew Essien a ranar 16 da watan Nuwamba a shekarar 1967 a jihar Akwa Ibom.

Etop Andrew ya fito ne daga karamar hukumar Nsit-Ubium dake jihar Akwa Ibom a kudu maso kudun tarayyar Najeriya, rahoton Daily Trust.

Etop ya rike matsayin tattara haraji

Daga cikin manyan matsayin da Etop Andrew Essien ya rike a hukumar kwastam akwai mataimakin kwanturola a kan harkar tatttara haraji.

A kan wannan matsayin ne kuma Etop ya rigamu gidan gaskiya yayin da yake bayani a majalisar wakilai a yau Litinin, 25 ga watan Yuni.

Kwastam na shirin kawo saukin abinci

A wani rahoton, kun ji cewa hukumar kwastam ta kasa ta yi alwashin kawo karshen matsalar boye abinci da ta addabi daukacin al'ummar Najeriya.

Kwastam ta ce a yanzu haka ta dauki masu matakai wanda za su kawo karshen matsalar domin kawo saukin rayuwa ga talakawan Najeriya.

Asali: Legit.ng

People are also reading