Home Back

Yayin Da Hare-hare A Kan Manoma Ke Ta’azzara… ‘Yan Nijeriya Miliyan 18.6 Na Fuskantar Matsananciyar Yunwa

leadership.ng 2024/4/29
IFAD

Masu ruwa da tsaki a bangaren harkokin noma a Nijeriya, na ci gaba da kokawa tare nuna damuwarsu a kan koma-bayan da ake samu kan harkokin abinci, sakamakon ci gaba da sace manoma ana garkuwa da su, wanda ya yi sanadiyyar manoman da dama suka kauracewa noman baki daya.

Binciken da LEADERSHIP ta gudanar ya tabbatar da kara tabarbarewar matsalar abinci a fadin kasa baki daya. Har ila yau, a wata sanarwa da Mukaddashin Shugaban Babbar Majalisar Koli ta Tattalin Arzikin Nijeriya (NESG), Ayanyinka Ayanlowo ya sanya wa hannu, a wajen taron kungiyar tattalin arzikin Nijeriya, an bayyana adadin ‘yan Nijeriyar da ke fama da karancin abinci wanda ya yi matukar karuwa daga miliyan 66.2 a 2023 zuwa miliyan miliyan 18.6, sannan ‘yan Nijeriya kimanin miliyan 43.7, sun fuskanci barazanar wannan yunwa a wannan wata na Maris da muke ciki.

Haka zalika, manoma da dama a wasu jihohi sun hakura da noma kwata-kwata, sakamakon yadda wannan harkoki na tsaro ke ci gaba da ta’azzara. Daga Jihohin Benuwe zuwa Sakkwato, Neja zuwa Filato, Kaduna zuwa Zamfara da kuma Katsina, abubuwan babu dadin ji.

Kamar yadda muka samu rahoto, a wannan shekara da muke ciki ta 2024, an yi asarar manoma kimanin 165 ta hanyar ta’addanci. A wasu bangarorin ma, wadannan ‘yan ta’adda jangali da haraji suke sanya wa wadannan manoma, wanda hakan yake tilasta musu zama cikin yunwa da rauni a gidajensu.

A Jihar Sakkwato, haka nan wadannan manoma suka yi ta kokawa kan biyan Naira miliyan uku a matsayin kudin fansa ga masu garkuwa da mutane. Har wa yau, a kwanan nan ne, Kungiyar Manoma ta Nijeriya (AFAN), ta tabbatar da rahoton SB Morgan da ke cewa, a Arewacin Nijeriya manoma na biyan ‘yan ta’adda har sama da Naira 100,000, domin samun damar zuwa gonakinsu su yi shuka ko yin girbi bayan amfanin gona ya nuna.

Haka zalika, a wani rahoto wanda kungiyar bincike ta Afirka ta yi, na nuni da cewa, duk manomin da bai bayar da hadin kai ba; shakka babu yana fuskantar barazanar yin garkuwa da shi tare da tashin hankali ko kuma kacokan a kwace masa amfanin gonarsa.

Sannan, a duk sanda wadannan ‘yan ta’adda suka yi yunkurin kisa, sai sun tayar da hankalin kowa tare da zub da jini. Guda daga cikin sabbin rahotannin kwanan nan, ya tabbatar da fadawar wasu mutane akalla su shida hannun wasu da ake zargin Fulani ne a Garin Kadarko da ke Karamar Hukumar Keana na Jihar Nassarawa.

A cikin Kadarkon, akwai mutane biyu da aka kai wa hari a Tse-Abir Azer ranar Juma’a, inda wasu manoma su ma ‘yan kabilar Tibi su uku, suka hadu da irin wannan iftila’i a ranar Lahadi; duk a unguwa daya.

Duk wadannan abubuwa da suke faruwa, su ne suka yi sanadiyyar hauhawar farashin da ake samu na kayan abinci a fadin wannan kasa. A watan Junairun 2024, an samu hauhawar farashin kayan abinci a Nijeriya zuwa kashi 35.41 cikin 100, maimakon kashi 33.9 cikin 100 a watan Disambar 2023.

Kodayake, Nijeriya ta koma shigo da kayan abinci daga kasashen waje, don bunkasa na cikin gida sakamakon matsalar tsaro da ake fama da ita, amma yawan adadin kudin kayan abincin da ake shigowa da su kamar yadda masana suka bayyana, ba abu ne da zai iya dorewa ba; domin kuwa binciken LEADERSHIP ya bankado cewa, Nijeriya ta kashe kimanin Naira tiriliyan 6.9 a shekara biyar kacal, wajen shigo da wadannan kayan abinci.

A wata kididdiga da Hukuma Kula da Kididdiga ta Kasa (NBS) ta fitar, adadin abincin da aka shigo da shi Nijeriya a shekarar 2022, ya haura Naira tiriliyan 1.9, idan aka yi la’akari da Naira tiriliyan 2 da aka kashe wajen shigo da wadannan kayan abinci a shekarar 2021. Haka nan, a shekarar 2020, Nijeriya ta shigo da kayan harkokin noma na kimanin tiriliyan 1.2, haka a shekarar 2019, kayan abincin da aka shigo da su sun haura na Naira biliyan 959.

Kazalika, Nijeriya ta shigo da kayan abinci na kimanin biliyan 857.6 a shekarar 2018. Kididdigar da aka samu ta yi nuni da cewa, daga shekarar 2018 zuwa 2022; tazarar da aka samu ta kayan abinci da ake shigowa da su, ta haura wanda ake fita da shi da kusan ninki uku. A nan, har da wasu daga cikin abubuwan da kasarmu ke nomawa da kyau, kamar irin su shinkafa, wadda aka fi mayar da hankali wajen kawo ta daga waje da kuma alkama wadda ita ma kodayaushe daga kasashen na waje ake kawo ta.

Har ila yau, masu ruwa da tsakin a kan harkokin noma, sun yi matukar bayyana takaicinsu, ganin cewa wannan harka ta noma ita aka fi sanin ‘yan Nijeriya da ita tun bayan samun ‘yancin kai a shekarar 1960. Amma tun bayan bayyanar man fetur a matsayin babbar hanyar samun kudin shiga a Nijeriya, sai aka yi watsi da sauran wasu bangarorin da ke rike da kasar kafin a samu man.

Bugu da kari, Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu, ya ba da tabbacin cewa, gwamnatinsa za ta farfado da sauran hanyoyin samun kudin shiga, domin ci gaban kasa da samun walwalar ‘yan Nijeriya. Haka nan, ya sake jaddada aniyar gwamnatinsa ta dakile batun shigo da abinci daga kasashen waje tare da yaki da karuwar matsalar yunwa a tsakanin al’umma. Kamar yadda sanarwar mai magana da yawun shugaban kasar, Ajuri Ngelale, ta bayyana, Tinubu ya jaddada aniyar gwamnatin tasa, ta kawo gagarumin sauyi da karancin abincin da ake fama da shi zuwa wadatuwarsa a cikin fadin kasa baki daya.

Har wa yau, masana harkokin noma; ba su yi kasa a guiwa ba, wajen ci gaba da jan hankalin gwamnatin tarayya, don yin hadin guiwa da masu ruwa da tsaki kan harkokin noma tare da zakulo muhimmancin tafiya tare da su, domin bunkasa wannan fanni na noma, musamman a wuraren da gwamnatin ta gaza.

Haka nan, kula tare da kare rayukan wadannan manoma na da matukar muhimmanci. Kamar yadda wani manomi a Jihar Benuwe, Pius Nwitete ya bayyana, lallai akwai bukatar gwamnati ta kula da tsaron rayukan manoma da dukiyoyin a fadin kasa baki daya. Ya kara da cewa, abin tashin hankali da takaici shi ne, yadda manoma suke gudu suna barin gonakinsu; sakamakon yadda ta’addancin ‘yan ta’adda ke ci gaba da yaduwa, musamman a yankunan Arewacin wannan kasa.

“A kasar da miliyoyin mutane ke fama da matsananciyar yunwa, kyautuwa ya yi a fi bai wa harkokin noma muhimmanci, ta hanyar karfafa wa manoma guiwa tare da ba su dukkanin gudunmawar da ta dace, domin samar da wadataccen abinci; musamman halin da aka tsinci kai na matsalar sauyin yanayi kan samar da abinci a duniya baki daya,” in ji shi.

Haka zalika, shi ma wani babban manomi, Umar Mohammed, wanda ke da babbar gona a Jihar Kano ya bayyana cewa, ba karamin abin takaici ba ne a ce, kadan daga cikin manoma ne ke iya samun damar yin amfani da motar tantan (tractors) da sauran kayan noma na zamani, wanda hakan ke ci gaba da kawo wa kokarin gwamnati cikas wajen shirinta na bayar da taraktocin da nufin karfafa harkokin noma.

A cewarsa, duba da yadda kayan aikin gona ke da matukar tsada tare da bai wa manoma rashin kwarin guiwa, kyautuwa ya yi a rika bai wa manoman tallafi, musamman idan aka yi la’akari da muhimmancin da suke da shi; wajen sama wa kasa abinci.

 
People are also reading