Home Back

Ɗandaudu, Bobirisky ya yi nadamar lika takardun naira da ya yi a wajen biki, ya roki sassauci a kotu

premiumtimesng.com 2024/5/12
Ɗandaudu, Bobirisky ya yi nadamar lika takardun naira da ya yi a wajen biki, ya roki sassauci a kotu

Kotu a Legas ta ɗaure fitaccen ɗandaudun nan mai suna Idris Okuneye da aka fi sani da Bobirisky bisa laifin la’anta takardun naira ta hanyar liki.

Hukumar yaki dacin hanci da rashawa ta kasa EFCC ta gurfanar da Bobrisky bisa laifuka shida da suka hada da cin zarafi da kuma karkatar da kudade.

A zaman da aka yi Suleiman wanda shine ya shigar da ƙara a madadin EFCC ya gabatar da shaida mai suna Bolaji Temitope wanda ya gabatar da bidiyon dake nuna Bobirisky yana lika wa wani mawaki Segun Johnson kudi a buki.

Temitope ya ce Bobirisky bayan ya ga bidiyon a ofishin su ya amsa laifukan da ake zargin sa da su.

Kotu ta yanke hukuncin tsare dandaudun a hannun hukumar EFCC har sai ranar 9 da za a yanke masa hukunci.

Rokon sassauci

A kotun Bobirisky ya roki sassauci tare da yin nadama kan laifukan da ake zarginsa da aikatawa.

Ya ce ba shi da masaniyar cewa laifi ne a Najeriya lika kudi a wurin buki amma ya yi alkawarin ba zai daki ba

“Ai bani da masaniya cewa akwai dokar da ta hana lika kudi a wurin buki amma idan aka bani dama, zan yi amfani da wannan laifi da na aikata domin wayar wa mutane kai game da dokar, domin mutqne da dama basu sani ba.

People are also reading