Home Back

Dortmund ta yi waje da PSG a Champions League

bbc.com 2024/5/19
Borussia Dortmund

Asalin hoton, Getty Images

Borussia Dortmund ta kai wasan karshe a Champions League, bayan da ta yi nasarar cin Paris St Germain 1-0 ranar Talata a Faransa.

Kungiyoyin sun je hutu ba ci, bayan da suka koma zagaye na biyu ne Dortmund ta ci kwallo ta hannun Mats Hummels.

A ranar Talata a makon jiya a wasan farko a daf da karshe a Jamus, Dortmunda ta yi nasara 1-0, kuma Niclas Fullkrug ne ya ci mata kwallon tun kan hutu.

Kenan Dortmund ta kai wasan karshe a gasar zakarun Turai ta bana da cin kwallo 2-0 gida da waje.

Wannan shi ne karo na hudu da suka hadu a bana a gasar zakarun Turai tsakanin Dortmunda da PSG, wadanda suka fara fuskantar juna a rukuni na shida.

Cikin Disambar bara Dortmund da PSG suka tashi 1-1 a wasa na biyu, bayan da PSG ta ci 2-0 a wasan farko a cikin rukuni cikin watan Satumba.

Kawo yanzu sun fafata a tsakaninsu sau takwas, inda Dortmund ta yi nasara uku da canjaras uku, yayin da PSG ta ci karawa biyu.

Dortmund ta dauki Champions League daya a 1996/1997, yayin da PSG har yanzu ba ta samu daukar kofin ba.

Kungiyar Jamus za ta jira wasan karshe da duk wadda ta yi nasara tsakanin Real Madrid da Bayern Munich ranar Laraba.

Ranar Talata ta makon jiya aka tashi 2-2 a Jamus a wasan farko na daf da karshe a gasar zakarun Turai tsakanin kungiyar Jamus da ta Sifaniya.

Real Madrid, wadda ta lashe La Liga na bana na 36 jimilla na fatan daukar Champions League na 15 jimilla.

Ita kuwa Bayern Munich, wadda ba ta dauki Bundesliga a bana ba tana da kofin zakarun Turai shida a tarihi.

A karshen kakar bana Kylian Mbappe, wadda ya lashe kofin duniya da tawagar Fransa, wanda bai taba lashe kofin zakarun Turai ba, zai koma Real Madrid.

People are also reading