Home Back

KAI TSAYE, Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 06/07/2024

bbc.com 2024/10/5

Rahoto kai-tsaye

Shugabannin ƙasashen Nijar da Mali da Burkina Faso na taro a Yamai

..

Asalin hoton, Getty Images

Nan gaba a yau ne shugabannin mlkin sojin ƙasashen Mali da Burkina Faso da Nijar za su gudanar da taronsu domin kammala ficewarsu daga ƙungiyar Ecowas, tare da sanar da kafa sabuwar ƙungiyar ƙawancen yankin Sahel.

Za a gudanar da taron ne a Yamai, babban birnin Jamhuriyar Nijar Nijar domin ƙaddamar da sabuwar ƙungiyar tasu a hukumance.

Taron ƙasashen uku na zuwa ne a jajibiren taron ƙungiyar ƙasashen yammacin Afirka ta ECOWAS, ko CEDEAO.

A watan Janairu ne ƙasashen uku suka sanar da ficewa daga Ecowas don nuna adawa da takunkumin da ƙungiyar ta ƙaƙaba musu.

Gwamnatocin sojan ƙasashen sun yanke hulda da Faransa, tsohuwar uwar gijiyarsu, inda yanzu suke ɗasawa da Rasha, da Turkiyya da kuma Iran.

People are also reading