Home Back

EFCC Ta Sake Maka Emefiele A Kotu Kan Wasu Sabbin Tuhume-tuhume 4

leadership.ng 2024/5/12
EFCC Ta Sake Maka Emefiele A Kotu Kan Wasu Sabbin Tuhume-tuhume 4

Tsohon Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Godwin Emefiele, na fuskantar sabbin tuhume-tuhume guda hudu daga EFCC.

EFCC ta zargi Emefiele da buga kudi Naira miliyan 684.5 ta hanyar kashe Naira biliyan 18.96.

EFCC, a sabbin tuhume-tuhumen da ta shigar a gaban babbar kotun tarayya, ta jaddada cewa tsohon gwamnan na CBN ya saba doka tare da karkatar da dukiyar jama’a a karkashin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari.

Ta kuma zargi Emefiele da cire Naira biliyan 124.8 daga asusun tara kudaden shiga (CRF) na tarayya ba bisa ka’ida ba.

Mai gabatar da kara daga tsagin EFCC, Rotimi Oyedepo, a cikin takarda mai kwanan wata 2 ga watan Afrilu, 2024 mai lamba: CR/264/2024, ya bayyana cewa za a gurfanar da tsohon gwamnan CBN a gaban mai shari’a Hamza Muazu na babbar kotun tarayya da ke Abuja.

Ana sa ran Emefiele ya kare kansa kan sabbin tuhume-tuhume guda hudu da suka da karya doka, cire kudi ba bisa ka’ida ba, almundahana da karkatar da dukiyar al’umma.

Tun a ranar 18 ga watan Nuwamba, 2023 ne, EFCC ta gurfanar da Emefiele a gaban kotu bisa tuhume-tuhume shida da suka shafi almundahana.

Ta kuma zarge shi da rashin bin ka’idar ofishinsa ta hanyar amincewa da kwangilar sayen motoci 43 da kudinsu ya kai Naira biliyan 1.2 daga shekarar 2018 zuwa 2020.

EFCC ta kuma gurfanar da tsohon shugaban CBN tare da wani Henry Omoile a gaban mai shari’a R.A. Oshodi na babbar kotun Ikeja, a Jihar Legas, a ranar Litinin, 8 ga watan Afrilu, 2024, bisa zarginsa da hannu a almundahanar Dala biliyan 4.5 da kuma Naira biliyan 2.8.

People are also reading