Home Back

Samoa: Sheikh Yahaya Jingir Ya Bayyana Matsayarsa Kan Yarjejeniyar, Ya Yi Gargadi

legit.ng 2024/10/6
  • Yayin da ake cece-kuce kan yarjejeniyar Samoa, Sheikh Sani Yahaya Jingir a ya bayyana matsayarsa kan lamarin
  • Sheikh Jingir ya yi fatali da yarjejeniya inda ya ce da Musulmi da Kirista da sauran masu addinai duk sun ce ba za su yi ba
  • Hakan ya biyo bayan sanya hannu a yarjejeniyar Samoa da Gwamnatin Tarayya ta yi da ake zargin ya kunshi auren jinsi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Plateau - Sheikh Sani Yahaya Jingir ya yi tsokaci kan yarjejeniyar Samoa da Gwamnatin Tarayya ta sanyawa hannu.

Shehin malamin ya yi fatali da yarjejeniyar inda ya ce ko kusa ba za a amince da wannan iya shege ba.

Sheikh Jingir ya yi tsokaci kan yarjejeniyar Samoa a Najeriya
Sheikh Sani Yahaya Jingir ya yi fatali da yarjejeniyar Samoa da aka sanyawa hannu. Hoto: Sheikh Sani Yahaya Jingir. Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sheikh Jjngir ya bayyana haka ne a cikin wani faifan bidiyo da Abdul'aziz Abubakar ya wallafa a shafin X.

Jingir ya ce da Musulmai da Kiristoci har ma da wadanda ba su da addini ba su amince da hakan ba.

Malamin ya bukaci Gwamnatin Tarayya ta janye wannan kudiri ba tare da bata lokaci ba saboda ba za su bari ba.

"Yanzu ga shi wani Minista ya je ya sanya hannu a boye za a ba su biliyoyin dala za a koma luwadi da madigo Allah ya tsare mu."
"Mu ƴan Najeriya Musulmai da Kiristoci har ma wadanda ba Musulmai ba kuma ba Kiristoci ba ba mu yarda ba."
"Waye ne zai shiga gaba ya amince da wannan doka bayan duk ƴan ƙasa ba su yarda ba."
"Ku shafe ta mu ba za mu yi luwadi da madigo ba, mu Musulmai mun ce ba za mu yi ba haka Kiristoci ma sun ce ba za su yi ba."

- Sheikh Yahaya Jingir

Samoa: Malamai sun dira kan Bola Tinubu

A wani labarin, kun ji cewa malaman addinin Musulunci da dama sun yi tsokaci kan yarjejeniyar Samoa da Gwamnatin Tarayya ta sanyawa hannu.

Malaman sun bayyana damuwa kan yarjejeniyar inda suka gargadi gwamnatin kan matsalolin da haka zai haifar a kasa.

Hakan ya biyo bayan sanya hannu a yarjejeniyar wanda Gwamnatin Tarayya ta ce ba shi da alaka da auren jinsi ko kadan.

Asali: Legit.ng

People are also reading