Home Back

Wani Magidanci Mukhtar Ya Fashe da Kuka a Kotu Bayan Matarsa Ta Ce Ya Daina Raya Sunnah

legit.ng 2024/6/29
  • Wata matar aure, Mutiat Adepoju ta roki kotu ta kashe aurenta saboda mijin ya daina kwanciyar raya sunnah da ita tun da ya kara aure
  • Sai dai magidancin mai suna Mukhtar ya fashe da kuka a harabar kotun kuma ya bayyana abubuwan da matarsa take yi har ga ƴaƴanta
  • Alkalin kotun ya ba su shawarar su yi la'akari da makomar ƴaƴansu idan suka rabu, kana ya ɗage zaman domin ba su lokacin sulhu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

jihar Kwara - Wani magidanci, Kolawole Mukhtar, ya gaza riƙe kansa yayin da ya amsa sammacin karar da matarsa ta kai tana neman ya sake ta a kotun yanki a Ilorin.

Mukhtar dai ya fashe da kuka a kotun da ke zama a babban birnin jihar Kwara yayin da aka masa bayanin matarsa, Mutiat Adepoju ta na son aurensu ya mutu.

Rikicin ma'aurata a Kotu.
Magidanci ya fashe da koka a kotun yanki a jihar Kwara Hoto: Court of Appeal Asali: Twitter

A rahoton hukumar dillancin labarai ta kasa (NAN), matar auren ta roƙi kotun ta kashe auren kuma ta damƙa kula da ƴaƴansu a hannunta tare da kuɗin ɗawainiya da su.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa matar ke neman saki?

Mutiat ta faɗawa kotun cewa mijinta ya cika ƙorafe-ƙorafe kuma ba ya sakin fuska sosai, kamar yadda Tribune Nigeria ta ruwaito.

“Ya daina sauke nauyin da ke kansa na miji a gare ni. Ba mu raya sunnah, watau saduwar aure. Mu kan samu saɓani na ma'aurata kuma mu shirya.
"Tun da ya kara aure ya daina kwanciya da ni bayan mun koma sabon gidan da muke ciki yanzu. Na gaji da faɗansa kuma a kowane dare ina jira ya ziyarce ni a ɗakina,” in ji ta.

Magidancin, wanda ya fashe da kuka, ya shaida wa kotun cewa matarsa ​​ba ta taimaka wa yaransu da aikinsu na makaranta kuma tana da girman kai.

"Sau biyar ta koma gidan iyayenta tun lokacin da na auri matata ta biyu kuma ni gaskiya na gaji da biko da rokon kada ta tafi,” inji shi.

Biyu daga cikin dangin mijin da suka halarci zaman kotun sun bukaci a ba su lokaci domin jaraba sasanta mata da mijin.

A nasa jawabin, Alkalin kotun, Mai Shari'a Ahmed AbdulKadir, ya shawarci ma'auratan da su yi la’akari da makomar ‘ya’yansu.

Daga nan ya dage sauraren karar har zuwa ranar 12 ga watan Yuli, 2024.

Wata mata ta haifu ƴan 4

A wani rahoton kuma wani dan Najeriya ya ba da labarin yadda wata mata ‘yar kasar ta haifi ‘ya’ya hudu bayan daukar dogon lokaci ta na jira.

A cikin labarin da ya bayar, ya bayyana cewa matar ta haifi ‘yan hudun ne a rana daya bayan ta shafe shekaru 18 ba haihuwa.

Asali: Legit.ng

People are also reading