Home Back

Zargin Karuwanci: Kotu ta aike da wasu ƴan Mata su 17 gidan gyaran hali

dalafmkano.com 4 days ago

Kotun Majistret mai lamba 51 ƙarƙashin mai Shari’a Hajara Safiyo Hamza, da ke jihar Kano, ta aike da wasu ƴan mata gidan ajiya da gyaran hali.

Tunda fari ƴan matan aƙalla su kimanin 17 an kama su ne a unguwar Sabon gari da ke jihar Kano, suna yawon ta zubar da kuma karuwanci.

Ƴan matan waɗanda aka gabatar da su a gaban kotun a wani yanayi na rashin kyan gani, sun bayyanawa kotun shekarunsu waɗanda suka kama daga shekara 18, zuwa 19, an kuma karanta musu zarge zargen da ake yi musu na yawan banza da karuwanci da kuma tayar da hankalin al’umma da shaye-shaye, inda suka amsa nan take.

Mai gabatar da ƙara Haziel, ya roƙi kotun da ta sanya wata rana dan a yi musu hukunci, domin iyayensu su bayyana a gaban kotun.

Kotun ta aike dasu gidan gyaran hali zuwa ranar 16 ga watan nan dan iyayensu su bayyana a gaban kotu, inda nan da nan suka ruɗe da Kuka

Wakilin Dala FM Kano, Yusuf Nadabo ya ruwaito cewar, yayin zaman wasu samari sun cika kotun da zummar su biya musu tara, sai dai kasancewar ba’a sanya su a hannun belin ba, a nan ne jami’in gidan gyaran hali Nasiru Dogarai ya tisa ƙeyarsu zuwa gidan gyaran hali.

People are also reading