Home Back

Ana Daf da Gudanar da Zabe, ’Yan Bindiga Sun Harbe Jigon Dan Takarar PDP

legit.ng 2024/7/6
  • Wasu ‘yan bindiga sun yi ajalin wani dan takarar karamar hukuma a jihar Enugu da ke Kudancin kasar, Hon. Ejike Ugwueze
  • Marigayin ya gamu da ajalinsa ne yayin da yake kan hanyar Neke Odenigbo da ke karamar hukumar Enugu ta Gabas a jihar
  • Rundunar ‘yan sanda a jihar ta bakin kakakinta, DSP Daniel Ndukwe ta tabbatar da faruwar lamarin a yau Asabar 8 ga watan Yuni

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Enugu – ‘Yan bindiga sun bindige wani dan takarar shugabancin karamar hukuma a jam’iyyar PDP a jihar Enugu.

Marigayin mai suna Ejike Ugwueze ya gamu da ajalinsa ne yayin da ya ke tuki kan hanyar Neke Odenigbo a karamar hukumar Enugu ta Gabas.

Lamarin ya faru ne a daren jiya Juma’a 7 ga watan Yuni a yankin inda maharan suka zagaye shi da bindige shi, cewar Daily Trust.

Ugwueze mamban jam’iyyar PDP na neman takarar shugabancin karamar hukumar Isi-Uzo da ke jihar.

Wannan na zuwa ne yayin da ake shirye-shiryen gudanar da zaben kananan hukumomi a jihar a watan Oktoba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahotanni sun tabbatar da cewa maharan sun tare motar dan siyasan kafin suka harbe shin an take tare da tserewa.

Wani mazaunin da ya bukaci boye sunansa ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce ana zargin kisan na da alaka da siyasa.

“Yana daga cikin masu karfi a cikin masu neman kujerar shugabancin karamar hukumar Isi-Uzo.”

Cewar majiyar

Kakakin erundunar ‘yan sanda a jihar, DSP Daniel Ndukwe ya tabbatar da faruwar lamarin a yau Asabar 8 ga watan Yuni.

Ndukwe ya tabbatar da cewa yanzu haka jami’ansu suna ci gaba da bincike domin zakulo wadanda suka aikta laifin.

‘Yan bindiga sun sace matar sarki

A wani labarin, kun ji cewa wasu ‘yan bindiga sun yi awon gaba da matar sarki a jihar Kaduna bayan kai wani hari.

Lamarin ya faru ne a yankin Ninzo da karamar hukumar Sanga a jihar inda suka kai farmaki fadar sarkin kafin aka dakile harin.

Rundunar ‘yan sanda ta tabbatar da bacewar matar sarkin bayan dakile harin inda ta ce ta baza jami’anta domin ceto ta.

Asali: Legit.ng

People are also reading