Jam'iyyaun masu matsakaicin ra'ayi ke da rinjaye a EU
Duk da gagarumin nasarar da jam'iyyar masu tsattsaurar ra'ayi suka samu a kasashen Faransa da Jamus da kuma Austria a zaben majalisar dokokin kungiyar Tarayyar Turai, har yanzu jam'iyyu masu matsakaicin ra'ayi ne ke kan gaba a majalisar dokokin ta EU. Sakamakon zabukan dai na ci gaba da nuni da cewa, jam'iyyar al'umma ta European People's Party (EPP), za ta tsaya a matsayinta na mafi rinjaye a majalisar.
Bisa dukannin alamu, shugabar hukumar gudanarwar kungiyar ta EU, Ursula von der Leyen na kan hanyar ci gaba da jagorancin kungiyar har zuwa shekarar 2029.
A makwanni masu zuwa ne, von der Leyen za ta nemi samun goyon bayan mafi yawan 'yan majalisar, domin amince mata a matsayin shugaba a karo na biyu.