Home Back

Yadda ƴan luwaɗi ke dabdala a ɓoye a Najeriya

bbc.com 2024/7/8

Asalin hoton, Demola Mako/The Fola Francis Ball

Yadda mutane suka riƙa tafiyar yanga a kan dandamali
Bayanan hoto, Yadda mutane suka riƙa tafiyar yanga a kan dandamali
  • Marubuci, Todah Opeyemi
  • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Lagos

Wajibi ne a ɓoye wurin da ake yin casun.

Wannan wani bikin ƴan luwaɗi ne a Najeriya, ƙasar da ta haramta alaƙa ko soyayyar masu jinsi ɗaya, kuma duk wani abu da zai nuna cewa mutum na yin irin wannan alaƙa ka iya jefa mutum cikin haɗari.

Wannan shagali na masu alaƙar jinsi ɗaya tamkar saɓa wa doka ne.

Waɗanda suka shirya taron tunawa da Fola Francis - matar da ta sauya jinsinta, wadda ta mutu a bara - ba su sanar da wurin da za a yi bikin ba sai da ya rage kimanin sa'o'i kaɗan gabanin lokacin bikin.

Amma hakan bai kashe wa mutum 500 da suka halarci wurin gwiwa ba, a kusa da bakin teku a birnin kasuwanci na Legas.

Wani wuri ne da aka katange, inda a kusa da shi aka zubar da karikitan motoci da suka lalace, wani wuri da ya yi ƙaurin suna wajen shirya casu.

Za a iya jin sauti na tashi, shiga cikin wannan wuri tamkar sauyawa ne daga rayuwar da aka fi sabawa da ita zuwa wata.

A nan ciki ne ƙungiyar masu alaƙar jinsi ɗaya ke dabdala, wannan wuri ne ke kange su daga sauran al'umma.

Saboda kare kansu, yawancin masu alaƙar jinsi ɗaya ko waɗanda suka sauya jinsinsu na amfani da kalmar 'queer' a turance domin bayyana kansu.

Suna ta shewa da fira, wannan tamkar murna ce ta kasancewa a wurin da suke da ƴanci.

Kowa ya sanya kaya da suka dace da taron.

Asalin hoton, Demola Mako/The Fola Francis Ball

Uyaiedu Ikpe-Etim (Hagu) da Ayo Lawson (Dama) su ne suka shirya cashewar
Bayanan hoto, Uyaiedu Ikpe-Etim (Hagu) da Ayo Lawson (Dama) su ne suka shirya cashewar

A cikin ɗakin taron, wanda aka kunna ƙwayayen lantarki marasa haske, za ka ga haske masu launuka daban-daban.

Mutane, waɗanda a waje ya zama musu dole su amince da al'ada game da yadda ya kamata namiji ya sa sutura, a nan sun samu ƴancin sanya hulunan ƙarin gashi da matsattsun kaya da kuma rangaɗa kwalliya a fuskokinsu.

Waɗanda suka shirya shagalin - Ayo Lawson da Uyaiedu - sun yi sha'awar hakan ne bayan halartar wani bidirin irin wannan.

A bara sun shirya irin wannan shagali domin murnar ƙaddamar da wani fim kan tarayyar jinsi guda, amma a wannan karo sun shirya bikin ne domin karrama Fola Francis.

Kafin mutuwar ta a cikin ruwa a bara, ta kasance wata ginshiƙi wajen shirya irin wannan shagali da ake yi a ƙarƙashin ƙasa.

Ta riƙa shiryawa da gayyatar masu tarayyar jinsi ɗaya zuwa manya-manyan shagulgulan da take haɗawa.

Asalin hoton, Demola Mako/The Fola Francis Ball

Wurin ya bai wa masu alaƙar jinsi ɗaya damar sakewa
Bayanan hoto, Wurin ya bai wa masu alaƙar jinsi ɗaya damar sakewa

Wata matar da ta sauya jinsinta ta shaida wa BBC cewa wannan tamkar mafarkinta ne "ya zama gaskiya."

Ta gudo ne daga wani yanki na arewacin Najeriya saboda ƙyamar da ake nuna mata, kuma marigayiya Fola Francis ce ta ba ta masauki.

Irin wannan ɓoyayyen bidiri na mutane masu alaƙar jinsi ɗaya za a iya cewa ya samo asali ne daga Amurka, lokacin da Amurkawa baƙaƙen fata suka riƙa shirya shagulgula a ɓoyayyun wuri, a tsakiyar ƙarni na 19.

Tun daga wannan lokaci ne wannan al'ada ta bunƙasa, kuma take faruwa a sassa daban-daban na Amurka da kuma wasu ƙasashe.

Asalin hoton, Demola Mako/The Fola Francis Ball

...
Bayanan hoto, Wadanda suka shiga gasa sun riƙa yin tafiyar yanga a kan dandamali

Asalin hoton, Demola Mako/The Fola Francis Ball

Wani namiji sanye da fatari a lokacin bikin
Bayanan hoto, Mutane sun riƙa tafi da shewa a lokacin da waɗanda suka fafata a gasa suke cashewa

A lokacin wannan shagali da aka shirya a gidan rawa na Fola Francis, mahalarta sun yi gasa a fannoni da dama, kamar ɓangaren kwalliyar jiki da fuska da kuma wanda ya fi iya saka kaya.

Ƴan kallo sun riƙa tafi suna shewa a lokacin da mutanen ke takawa a kan dandamali.

Manufar waɗanda suka shirya dabdalar ita ce: su samar da wuri mai aminci inda kowa zai yi abin da yake so duk kuwa da hali na fargaba da irin waɗannan mutane ke ciki.

Wani ɗan luwaɗi ya shaida wa BBC cewa: "Ban iya sakewa ɗari bisa ɗari. Za a iya gano mutum cikin ƙanƙanin lokaci". Ya bayyana wa BBC yadda ƴansanda suka tarwatsa wani taro na ƴan luwaɗi a lokutan baya.

Asalin hoton, Demola Mako/The Fola Francis Ball

Alƙalan gasar da aka gudanar a lokacin shagalin
Bayanan hoto, Ashley Okoli (Hagu) da Ozzy Etomi (Dama), daga cikin sanannun mutane a Najeriya, sun taimaka a lokacin shagalin ta hanyar zama alƙalan gasar da aka yi

To amma waɗanda suka shirya taron sun yi bakin ƙoƙarinsu domin samar da yanayin da mahalarta za su saki jiki.

Wasu daga cikin matakan da suka ɗauka sun haɗa da ɗakin sauya kaya, ta yadda waɗanda ke son su saka kayan da suke so za su samu damar hakan ba tare da sun fuskanci tsangwama ba a kan hanyarsu ta zuwa wurin.

Sun kuma ƙulla yarjejeniya da wasu kamfanonin samar da tsaro waɗanda suka amince da cewa kowa na da ƴancin zama abin da yake so.

People are also reading