Home Back

Shugabannin Arewa sun caccaki na kudu kan neman sakin Nnamdi Kanu

bbc.com 3 days ago
.

Asalin hoton, Getty Images

Wasu kungiyoyin farar hula na yankin areawacin Najeriya sun jaddada cewa kotu ce kawai ya kamata a bari ta yanke hukunci kan makomar jagoran haramtacciyar kungiyar nan mai fafutukar neman kafa jamhuriyyar Biafra ta IPOB a yankin kudu maso gabashin kasar, Nnamdi Kanu ba gwamnatin tarayya ba.

Wannan martani ya biyo bayan kokarin da wasu gwamnoni da 'yan majalisar dokokin tarayya na shiyyar kudu maso gabashin Najeriyar wato yankin al'ummar Ibo ke yi na neman gwamnatin Najeriyar ta saki jagoran na IPOB, duk da kasancewar yana fuskantar shari'a a gaban kotu, bisa zarge-zargen aikata laifuka da suka shafi cin amanar kasa.

Shugaban gamayyar ƙungiyoyin arewacin Najeriya, wato CNG Jamilu Aliyu Charanchi ya ce " kowa na sane da yadda aka halaka mutane tare da ƙona dukiyoyin miliyoyin nairori na mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba, wanda kuma kowa ya san cewa Nnamdi Kanu da yaransa ne ke aikatawa"

''Duk wanda ya san abun da yake yi, kuma ya ke son ci gaban ƙasarsa, ba za ka same shi yana maganar sakin Kanu ba, a dai dai lokacin da har yanzu mutanensa na ci gaba da miyagun ayyuka, wannan cin mutunci ne ga gwamantin Bola Tinubu, da ita kanta APC. a cewarsa.

''Ya ce ''Har yanzu mutumin nan bai taba fitowa ya nemi yafiyar iyalan sojojin da ya kashe, da masu dukiyoyin da ya barnatar musu hakkinsu ba, yan uwansa na ci gaba da kashe jama'a''

Shuhugaban kuniyar ta ƴan Arewa ya ce yanzu ta tabbata kenan zargin da mutane ke yi cewar ba Nnamdi Kanu ne kaɗai ke aikata irin waɗannan laifuka, da goyon bayan shugabanin yankin da ya futo, tunda babu yadda za a yi ka ce za ka nemi a saki mutumin da kasan yana aikata laifi, in ba don kana goyan bayansaba"

Shugaban gamayyar ƙungiyoyin ya ce laifin da ake zarign Nnamdi Kanu da aikatawa na samar da dakarun sojojin a yankinsu har su ayyana ficewa daga Najeriya laifuka ne na cin amanar kasa ba wai gwagwarmaya ba.

"Wacce irnin gwagwarmaya ce wannan, wadda ta wuce tashin hanakali, su futo cikin ƙasa su ce ga sojojinsu, su kashe al'umma, su sanya dokar da ta ci karo da ta Najeriya ko kuma su ce kowa ya zauna a gida duk wanda ya fito za a kashe shi?'' inji shi.

Cikin abubuwan da Shugaban gamayyar ƙungiyoyin arewacin Najeriya, wato CNG Jamilu Aliyu Charanchi ya lissafo abin da suke son a yi wajen ɗaukar mataki sun haɗa da cewa lallai ne gwamanti ta bar kotu ta yankewa Nnamdi Kanu hukucin lafin da ake zargin sa da aikatawa kamar yadda kundin tsarin mulkin ƙasar ya tanada.

Haka kuma, gwamanti ta futo fili ta gargaɗi shugabanin da ke yankin kudu maso gabashin Najeriya musamman yan siyasar yankin su sani cewar baza su iya yin katsalanda a cikin sha'anin da ya safi ƙasa baki ɗaya da kuma shari'a ba.

Sannan Jamilu Aliyu Charanchi ya ce sakin Nnamdi Kanu babu wani sauyin da zai haifar face ma sake tsananta rashin tsaro a yankin kudu maso gabashin Najeriyar domin bai sauya hali ba.

A shekarar 2015 ne aka kama Nnamdi Kanu amma ya tsere daga Najeriya a 2017 bayan an bayar da shi beli, wanda daga bisani bayan kamoshi daga ƙasar Kenya, gwamantin Najeriya ta ci gaba da tsare shi a 2021, bayan da aka tuhume shi da zargin ta'addanci da kuma cin amanar kasa.

People are also reading