Gwamnatin Tarayya ta Kaddamar da Jigilar Kaya a Jirgin Kasan Tashar Tsandauri da ke Kano
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano- Gwamnatin tarayya ta kaddamar da jirgin farko na kaya daga tashar tsandauri ta Dala Inland da ke Kano zuwa tashar APM ta Apapa a Legas.
Da yake kaddamar da tashar, ministan sufuri Sanata Said Ahmad Alkali, shigowa da fitar da kayayyaki zuwa Arewa zai yi sauki sosai.
A shafinsa na facebook, ministan ya bayyana yakinin samun bunkasar kasuwanci ga mazauna yankin tashar tsandaurin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ministan sufuri, Sanata Sa'id Ahmad Alkali ya bayyana cewa an yi gagarumar nasara wajen fara jigilar kaya daga jirgin kasan tashar tsandauri ta Kano zuwa Legas.
Ministan ya ce an yi nasarar sufurin kwantena 40 na kaya daga Kano zuwa tashar Apapa da ke Legas a cikin 'yan kwanaki kadan.
Ya ce gwamnati ta na iya kokarinta wajen zamanantar da ayyukan sufuri, shi ne ma ya sa ta dauki gabarar gyara layin dogo na Kaduna-Kano, da ginin layin dogo daga zuwa Maradi.
A baya mun kawo mu ku labarin cewa Ministan Sufuri, Sa'id Ahmad Alkali ya bayyana cewa layin dogon da gwamnati ta gina daga Kano zuwa Legas zai fara jigila a wayan Yuni.
A yadda gwamnati ta dauko aikin, za a hade shi ne da tashar jiragen ruwa da kuma tashar tsandauri da ke Zawaciki a jihar Kano domin saukaka shigowa da fitar da kaya.
Asali: Legit.ng