Home Back

Tsohon Shugaban APC Ya Fallasa Wanda Ya Jawo Ake Binciken Gwamnatin El Rufai

legit.ng 2024/7/1
  • Salihu Muhammad Lukman ya na ganin babu inda Bola Ahmed Tinubu da Uba Sani za su kara motsawa a tafiyar siyasa
  • Tsohon mataimakin shugaban na APC yana ganin fadar shugaban kasa tana da hannu wajen binciken Nasir El-Rufai a Kaduna
  • A wata wasika, Salihu Muhammad Lukman ya fadawa gwamnan Kaduna cewa an kama hanyar ganin bayan mulkinsu a 2027

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Kaduna - Salihu Muhammad Lukman ya yi kaca-kaca da gwamnan jihar Kaduna, Malam Uba Sani, har ya ce ba zai zarce a ofis ba.

Tsohon mataimakin shugaban na jam’iyyar APC yana ganin Bola Tinubu da Uba Sani ba za su yi nasarar komawa kujerunsu a 2027 ba.

Bola Tinubu da Gwamna Uba Sani
El-Rufai: Salihu Lukman ya soki Bola Tinubu da Gwamna Uba Sani a APC Hoto: Kabiru Garba Asali: Facebook

Lukman ya kare gwamnatin El-Rufai

The Guardian ta rahoto Salihu Muhammad Lukman yana magana a kan rikicin da Mai girma gwamna Uba Sani yake yi da Nasir El-Rufai.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

‘Dan siyasar yana ganin cewa gwamnan Kaduna yana taya fadar shugaban kasa yakar tsohon gwamnan ne da sunan binciken mulkinsa.

A wata wasika da ya rubuta a ranar 13 ga watan Yuni, Salihu Lukman ya ce tun yanzu an fara shirin kifar da Tinubu da gwamnatin Uba.

Watakila APC za ta rasa zaben 2027

A takardar, Lukman ya gargadi Uba Sani, ya ce ko da ya dace, shekaru bakwai suka rage masa kamar yadda Daily Post ta rahoto a jiya.

Idan har APC ba ta shiga taitayinta ba, ‘dan siyasar ya ce za su yi bakin kokarinsu wajen ganin sun ga bayan jam’iyyar a takarar 2027.

Vanguard ta rahoto Lukman yana zargin Ibrahim Zailani da hannu a binciken gwamnatin El-Rufai tare da taimakon fadar shugaban kasa.

Wadanda aka aikawa wasikar sun hada Mallam Nasir El-Rufai, Ramalan Yero, Rt. Hon. Abbas Tajudeen, B. A. Law-al da Hon. Garba Datti.

Haka kuma an hada da Suleiman Hunkuyi, Yusuf Mairago, Lawal Samaila Yakawada, Bashir Abubakar Alhaji da Mohammed Sani Dattijo.

Uba Sani da gwamnatin Nasir El-Rufai

Ana da labarin ana ganin gwamnatin Uba Sani ta taso Nasir El-Rufai a gaba duk da alakar da ke tsakanin mutanen da suke tsofaffin abokai.

Shehu Usman Adamu bai ganin rigima ake yi a Kaduna, ya ce gwamna da mai gidansa aminai ne har yau, sunnar siyasa ta gaji haka.

Asali: Legit.ng

People are also reading