Home Back

RA’AYIN PREMIUM TIMES: Masu raji da ƙumajin kafa kafa ƙasar Yarabawa zalla ku shiga taitayin ku

premiumtimesng.com 2024/5/19
RA’AYIN PREMIUM TIMES: Masu raji da ƙumajin kafa kafa ƙasar Yarabawa zalla ku shiga taitayin ku

Gungun wasu tsageru kuma taƙadarai masu suna Ominira Yoruba 22, sun afka cikin garin Ibadan, inda suka yi ƙoƙarin mamaye Sakateriyar Gwamnatin Jihar Oyo, a ranar 13 ga Afrilu.

Babban muradin su shi ne yin amfani da ƙarfin tsiya domin su ƙwace Majalisar Dokokin Jihar Oyo, Gidan Gwamnatin Oyo da Sakateriyar Gwamnatin Jiha, inda daga nan kuma sai su ayyana kafa ƙasar Yarabawa Zalla, kenan za su ce sun ɓalle daga Najeriya.

Wannan babban laifi ne na cin amanar ƙasa, kuma ganganci ne ba ƙarami ba. Amma jami’an tsaro da suka haɗa da sojoji, ‘yan sanda da Amotekun sun fi ƙarfin su, domin sun mamaye su, an damƙe na damƙewa.

Lallai nan da tsawon lokaci mai nisa za su kasance cikin rayuwar ɗanɗana sakamakon laifin da suka aikata.

Sun zaɓi fara tawayen na su a birnin Badun, saboda can ne Hedikwatar Firimiyan Yamma, a zamanin Jamhuriya ta Farko.

Waɗannan tsagerun fa don rashin kunya da ƙarfin hali, har artabu suka yi jami’an tsaro. Kuma sojoji sun ƙwato makamai da albarusai da kayan sojoji da wayoyin oba-oba, layu da guraye, karhuna da tarkacen tsatsube-tsatsube sai kuma tutar ‘ƙasar Oudua da sauran su.

Wata Kotun Majistare da ke Ibadan dai a ranar Laraba ta bayar da umarnin ci-gaba da tsare mutane 29 a gidan kurkuku.

Kwamishinan ‘Yan Sandan Oyo, Hamzat Adebola, ya ce ana ci gaba da binciken gano waɗanda ke ɗaukar nauyin tsagerun.

To amma dai akwai wata mata da ke zaune a Amurka, mai suna Modupe Onitiri-Abiola, wadda ta yi iƙirarin cewa tsahuwar matar marigayi MKO Abiola ce, wanda ya lashe zaɓen 12 ga Yuni, 1992 da aka soke a lokacin. Wannan mata ta bayyana kan ta da kan ta, inda a cikin wani bidiyo da aka watsa mai ɗauke da inda take cewa: Ranar 12 ga Afrilu, 2024 ta fara kasancewa ranar kafa ƙasa mai ‘yanci.”

Ya zama wajibi hukumomin tsaro su gaggauta kama dukkan masu hannu a wannan yunƙuri, kuma a gurfanar da su, tare da tabbatar da an hukunta su.

Yin hakan zai zama babban darasi ga duk wasu masu mummunan mafarkin ɓallewa a ko’ina suke cikin sassan ƙasar nan.

Masu bibiyar tarihin Najeriya na sane da yadda aka fara fama da irin wannan tsagerancin tun a cikin Fabrairu, 1977, inda Isaac Adaka Boro ya ayyana yankin Neja Delta matsayin ƙasa mai ‘yanci, ta hanyar kafa dakarun balantiya. Amma dai an gaggauta murƙushe shi cikin ‘yan kwanaki kaɗan.

Bayan nan kuma sai yunƙurin kafa ƙasar Biafra, wanda ya yi munin da ya kai ga yin juyin mulki da kuma wani juyin mulki, har dai ta kai ta Yaƙin Basasa, bayan da Laftanar Kanar Chukwuemeka Odumegwu-Ojukwu ya ayyana ɓallewa ya ce ya kafa Jamhuriyar Biyafara.

Wannan ya haddasa yaƙin basasa data 1967 zuwa 1970, yaƙin da ya haifar da asarar miliyoyin jama’a.

Ganin irin mummunar asalar miliyoyin rayuka da ɗimbin dukiya a yaƙin basasa, sai ake ganin ba za a sake samun wasu wawaye su sake ganganci ko wautar hanƙoron sake ɓallewa ba.

Amma hakan bai hana wasu masu kunnen-ƙashi sake bayyana ba, irin su MOSOP, OPC, MASSOB, IPOB da kuma ta yanzu mai kiran kan ta Yoruba Nation.

A ɗaya gefen kuma ga Boko Haram masu ƙumajin kafa Daular Musulunci, waɗanda bala’in da suka haifar a Najeriya ba ya misaltuwa.

To ita dai Onitiri-Abiola irin su Nnamdi Kalu da Simon Ekpa ne, wanda ke zaune a Finland.

Ya zama wajibi hukumomi su tashi su nemi Amurka ta kama ta, ta turo ta Najeriya, domin a hukunta ta.

Dama kuma Shugaban Ƙasa Bola Tinubu a ranar Laraba ya bayyana cewa, “za mu tarwatsa dukkan masu ƙoƙarin su tarwatsa Najeriya. Sai hukunci ya hau kan su, kuma ba za mu sare ko gajiya ba har sai mun kai ga hukunta su.”

People are also reading