Home Back

Barka da Sallah: Ganduje Ya Bayyana Abin da 'Yan Najeriya Ya Kamata Su Yi Wa Tinubu

legit.ng 2024/5/15
  • Shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje ya taya al'ummar Musulmai murnar zuwan lokacin bikin ƙaramar Sallah
  • Ganduje ya buƙaci ƴan Najeriya da su ci gaba da marawa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu baya
  • Tsohon gwamnan na jihar Kano ya yi nuni da cewa shugaban ƙasan na yin bakin ƙoƙarinsa domin tsamo mutane daga halin wahalar da suke ciki a yanzu

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Abdullahi Umar Ganduje, shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, ya buƙaci ƴan Najeriya su marawa Shugaba Bola Ahmed Tinubu baya.

Ganduje ya yi nuni da cewa shugaban ƙasan yana yin duk mai yiwuwa domin tsamo su daga halin wahala da suke ciki a yanzu, jaridar The Punch ta kawo rahoton.

Ganduje ya yi kira ga 'yan Najeriya
Ganduje ya bukaci 'yan Najeriya su marawa Tinubu baya Hoto: @OfficialAPCNg Asali: Twitter

Ganduje ya kuma buƙaci al'ummar Musulmai da su yi amfani da darussan da suka koya a watan azumin Ramadan wajen gudanar da rayuwarsu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban na jam'iyyar APC ya bayyana hakan ne a cikin saƙon barka da sallah da sakataren yaɗa labaransa, Edwin Olofu ya fitar a birnin tarayya Abuja, rahoton Solace Base ya tabbatar.

Wane kira Ganduje ya yi wa ƴan Najeriya?

A yayin da ya aminta da cewa sauyi na zuwa da ɗumbin ƙalubale, tsohon gwamnan na jihar Kano ya buƙaci ƴan Najeriya su ƙara haƙuri da Tinubu domin kai ƙasar nan zuwa kan tudun mun tsira.

A kalamansa:

"Ina kira ga dukkanin ƴan Najeriya ba tare da la'akari da jam'iyyunsu ba, da su marawa shugaban ƙasanmu baya. Duk mai hankali ya san cewa Shugaba Tinubu ya ɗauki muhimman matakai domin farfaɗo da tattalin arziƙinmu, kuma kwalliya ta fara biyan kuɗin sabulu."
"Abin da muke buƙata yanzu shi ne mu marawa gwamnatin tarayya baya domin kawo sauyi a ƙasar nan."

Ganduje ya kuma yi kira kan cewa darussan da aka koya a cikin kwanaki 30 na azumi bai kamata a yi watsi da su ba.

Ya kuma buƙaci al'ummar Musulmai da su ci gaba da yi wa shugaban ƙasan addu'o'i.

Ganduje zai gurfana a kotu

A wani labarin kuma, kun ji cewa wata babbar kotu a jihar Kano ta sanya ranar da za ta gurfanar da tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje, a gabanta.

Za a gurfanar da Ganduje, matarsa da wasu mutum shida kan zargin cin hanci da rashawa da karkatar maƙudan kuɗaɗe.

Asali: Legit.ng

People are also reading