Home Back

Idan Isra’ila Ta Kai Wa Iran Hari Ba Za Mu Goya Mata Baya Ba – Amurka

leadership.ng 2024/5/17
Idan Isra’ila Ta Kai Wa Iran Hari Ba Za Mu Goya Mata Baya Ba – Amurka

A yayin da Isra’ila ke nazarin yadda za ta mayar da martani kan harin da Iran ta kai mata a karshen mako, Amurka ta bayyana cewa babu ruwanta idan har kasar ta zabi daukar fansa ta hanyar soji.

Sakon na Amurka da ba a saba ganin irinsa kan babbar aminiyarta da ta ke bai wa taimakan soji fiye da kowace kasa a duniya, ta ce ba za ta shiga rikicin Iran da kuma Isra’ila ba.

Bayan watanni da Isra’ila ta yi na daukar fansa a Gaza, duk da suka daga Amurka da sauran kawayenta da ke cewa ayyukan sojinta sun wuce gona da iri.

Gwamnatin Biden ta bayyana karara cewa, tana tsoron yaki mafi girma ya barke a Gabas ta Tsakiya.

“Mun yi imanin Isra’ila na da ‘yancin daukar mataki don kare kanta, amma wannan wani salo ne na siyasa,” in ji wani babban jami’in fadar White House ga manema labarai jim kadan bayan kawo karshen harin na Iran. ”

Da wani dan jarida ya tambaye shi ko Amurka za ta taimaka wa Isra’ila wajen tunkarar hare-haren soji, nan take ya ce a’a.

Amurka ta ce tuni ta isar da wannan sakon kai tsaye ga manyan jami’an Isra’ila a wata ganawar sirri ta wayar tarho da ta gudana tsakanin sakataren tsaro Lloyd Austin da ministan tsaron Isra’ila Yoav Gallant.

Harin da Iran ta kai kan Isra’ila da yammacin ranar Asabar ya sha kakkausar suka daga shugabannin duniya, ciki har da jami’an Amurka wadanda da farko suka yi tunanin kasar ta yi amfani da makamai masu linzami guda 12.

Harin dai, Iran ta kira shi a matsayin ramuwar gayya bayan harin da Isra’ila ta kai ofishin jakadancinta da ke Damascus na kasar Syria.

People are also reading