Home Back

Everton ta kammala ɗaukar Ndiaye daga Marseille

bbc.com 2024/10/6
Iliman Ndiaye

Asalin hoton, Everton

Everton ta kammala ɗaukar ɗan wasan tawagar Senegal, Iliman Ndiaye daga Marseille kan yarjejeniyar kaka biyar kan £15m.

Mai shekara 24, ya koma Marseille daga Sheffield United a bara.

Ndiaye ya ci ƙwallo hudu daga karawa 46 a kakar da ta wuce, ya taimakawa ƙungiyar Faransa ta kai daf da karshe a Europa League.

Sheffield United ta karɓi £20m kuɗin Ndiaye, bayan cin ƙwallo 14 da bayar da 11 aka zura a raga da ƙungiyar ta samu gurbin shiga Championship a 2022-23.

Sheffield ta sayi Ndiaye daga karamar ƙungiya, Boreham Wood a 2019.

Ndiaye ya zama na uku da Everton ta ɗauka a bana, bayn Jack Harrison da ya kammala buga wasannin aro a Leeds United da kuma Tim Iroegbunam daga Aston Villa.

People are also reading