Home Back

KAFADA ku kula da mutanen da ku ke baiwa haya ko sayar da fili ko Gida – Gwamnatin Kano

dalafmkano.com 2024/7/6

Gwamnatin jihar Kano ta buƙaci masu hada-hadar Kasa da Gidaje, da su ƙara himma wajen kula da mutanen da suke bai wa hayar Gidaje ko kuma sayar musu, domin gujewa bada hayar ko kuma sayar wa masu laifi, wanda hakan ka iya taimaka wajen magance matsalar tsaro a ɓangaren.

Kwamishinan ma’aikatar kasuwanci da zuba hannun jari na jihar Kano Alhaji Adamu Aliyu Kibiya, ne ya bayyana hakan yayin ziyarar da tawagar ƙungiyar masu hada-hadar Ƙasa da sayar da Gidaje da kuma bayar da hayar su ta jihar Kano KAFADA, suka kai masa ranar Alhamis a ofishin sa.

Kibiya, ya kuma ce kula da waɗanda za su rinka bai wa hayar gidajen da kuma siyar musu zai taimaka wajen magance matsalar tsaro a sassan jihar Kano da ma ƙasa baki ɗaya.

Da yake nasa jawabin shugaban kungiyar ta KAFADA, Alhaji Isah Jibril Isah, mai lakabin Kaci-Kasa, ya ce sun kai wa kwamishinan ziyarar ne, domin gabatar masa da kungiyar, da kuma tabbatar masa da hadin kan da za su bashi domin kara bunkasa harkokin kasuwanci a faɗin jihar Kano.

“A shirye kungiyar mu take wajen tabbatar da mambobin mu suna kula da irin mutanen da za su bai wa hayar gida ko kuma sayar musu, domin bada gudunmawar mu ga gwamnati wajen magance matsalar tsaro a jihar Kano, da ma ƙasa baki ɗaya, “in ji shi”.

Alhaji Isah Jibril Isah, ya kuma kara da cewa za su ci gaba da kokari wajen
tsaftace harkokin hada-hadar kasa da sayar da gidaje da bada hayar su, tare da ƙoƙarin ɗaukar mataki akan gurɓatattun mutanen da suke kiran kan su a matsayin dillalai suna
damfarar mutane.

People are also reading