Home Back

Batun Musanya Sunan Titin Murtala Da Na Soyinka, Ba Gaskiya Ba ne – Minista

leadership.ng 2024/7/4
Amurka

Gwamnatin Tarayya ta ƙaryata ji-ta-ji-tar da ake yaɗawa cewa, ta canza sunan Titin Murtala Muhammed da ke Abuja zuwa Titin Wole Soyinka.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mataimaki na musamman kan Harkokin yaɗa Labarai ga Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Rabiu Ibrahim ya fitar a ranar Litinin.

A cewar sanarwar, ta bakin Ministan Yaɗa Labarai da wayar da kai, Alhaji Mohammed Idris, ta ce, Gwamnati ba ta da wani kuduri na sauya sunan Titin Murtala Muhammed.

A ranar 4 ga watan Yuni, 2024 ne Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya ƙaddamar da wata sabuwar hanya a Birnin Tarayya, Abuja, wadda aka yi wa laƙabi da “Titin Arterial N20”, wadda ta haɗa Katampe zuwa Jahi ta kuma haɗa babbar hanyar Arewa (Murtala Muhammed Expressway) zuwa babbar hanyar Arewa (Ahmadu Bello Way).

A yayin ƙaddamarwar, Ministan Babban Birnin Tarayya, Barista Nyesom Wike, ya bayar da shawarar a raɗa wa sabon titin na ‘Arterial N20’ sunan Farfesa Wole Soyinka, shawarar da Shugaban Ƙasa ya amince da ita.

Saboda haka, sabon titin ‘Arterial N20’ ne aka sanya wa sunan Soyinka, ba Titin Murtala Muhammed ba.

Shi Titin Murtala Muhammed yana ci gaba da riƙe asalin sunansa, wanda karramawa ce ga mai girma tsohon Shugaban Ƙasa, Janar Murtala Ramat Muhammed.

Idris ya buƙaci jama’ar ƙasa da su yi watsi da rahotannin ƙarya da ke cewa wai an sauya sunan titin, rashin fahimta ce ko kuma “ƙage-ƙage ne kurum marasa tushe”.

People are also reading