Home Back

Harin ta'addanci a Jamhuriyar Benin ya hallaka sojojinta 7

dw.com 2024/7/2
Hoto: Sia Kambou/AFP

Wani harin ta'addanci a Jamhuriyar Benin ya hallaka sojojin kasar 7, a wurin shakatawa da yawon bude ido na Pendjari da ke arewacin kasar, kamar yadda hukumokin tsaron kasar suka sanar a Alhamis din nan.

Majiyar tsaron ta ce harin na kwanton bauna ne daga kungiyoyin da ke da alaka da al Qaeda a IS, a yankin Tanguieta mai kusanci da iyakar Burkina Faso da kuma Jamhuriyar Nijar, wadanda ke fama da hare-haren ta'addanci.

Ko a cikin watan Afirilun da ya gabata ma harin ta'addancin ya yi sanadiyyar mutuwar mutane uku, a kusa da iyakar Benin din da Jamhuriyar Nijar.

People are also reading