Home Back

'Yan gudun hijira 38 sun rasu a kogin Djibouti

dw.com 2024/5/16
Kungiyar kula da kaurar jama'a ta duniya IOM
Kungiyar kula da kaurar jama'a ta duniya IOM

A kalla 'yan gudun hijira 38 ne suka rasu bayan da jirgin ruwan da suke ciki ya kife a gabar kogin Djibouti a cewar kungiyar kula da kaurar jama'a ta duniya IOM.

Kungiyar ta ce wasu mutanen shidda sun bace ba a gan su ba, sai dai ana kyautata zaton su ma sun mutu. Sai dai kuma an sami nasarar ceto mutane 22.

A kowace shekara dubban 'yan gudun hijira ne suke barin yankin kahon Afirka, yawancinsu daga Habasha da Somalia inda suke kokarin zuwa kasashen yankin tekun fasha  a cewar Yvonne Ndege mai magana da yawun kungiyar kula da kaurar jama'a ta duniya.

People are also reading