Home Back

Abu huɗu da majalisar jihar Kaduna ke binciken gwamnatin Nasiru El-Rufa'i a kai

bbc.com 2024/5/7
..

Asalin hoton, NASIR ELRUFA'I/FACEBOOK

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta ce ta fara gudanar da bincike kan yadda tsohon gwamnan jihar Malam Nasiru El-Rufai ya karɓo tare da tafiyar da basuka na tsawon shekaru takwas da ya yi yana mulkin jihar.

A baya-bayan nan ne dai gwamnan jihar mai ci Malam Uba Sani ya ɓara cewa gwamnatin nasa ba ta iya gudanar da wasu muhimman abubuwa na yau da kullum da suka haɗa da biyan ma'aikata albashi sakamakon tarin bashin da ke kan jihar.

Wasu alƙaluma da hukumar da ke gudanar da harkokin bashi a Najeriya ta fitar, sun nuna cewa Kaduna ce jiha ta biyu da bashi ya yi wa katutu bayan jihar Lagos a Najeriya.

Majalisar ta bakin shugaban kwamitin da ke jagorantar binciken ta ce lamarin zai iya kai wa ga neman tsohon gwamnan, Nasir El-rufai ya gurfana a gaban majalisar.

Me za a bincika?

Ɗaya daga cikin 'yan majalisar jihar ta Kaduna kuma mamba a kwamitin da ke wannan bincike, Hon Alhassan Mohammed Ikara ya ce :

"Gwamnatin da ta shuɗe ta ciyo basuka da yawa domin gudanar da ayyukan raya ƙasa. To amma bayan da ta wuce sai mu ka ga ta tafi ta bar baya da ƙura domin waɗannan basuka sun bar baya da ƙura inda yanzu a halin da ake ciki gwamnatin jihar Kaduna ba ta iya biyan albashi har sai an ci bashi." In ji Hon Alhassan.

Da aka tambayi Hon Alhassan kan cewa me ya sa wasunsu da suka kasance a majalisar lokacin gwamnatin tsohon gwamnan ba su hana ba? Sai ya ce

"Ai yanzu ne ake cire basukan da gwamnatin ta baya ta ciyo. To shi ya sa duk muke da damuwa a kan wancan bashi da aka ciyo." In ji Hon Alhassan.

Abu huɗu da muke bincike a kai'

Hon Alhassan Mohammed Ikara ya ce ba wani abu ba ne ya sa muke son ƙaddamar da wnanan bincike illa domin "muna son sanin wasu abubuwa guda huɗu".

  • Na farko shi ne ko an bi ƙa'ida wajen bashin da aka ciyo?
  • Da kuma aka ciyo bashin ko an yi abin da doka ta tanadar kamar kai wa majalisa ta sahhale wa gwamnati cin bashin?
  • Na uku aikace-aikacen da aka karɓo bashin domin yi su ne aka yi?
  • Na huɗu za ka ga 'yan kwangilar da suka yi aikin har yanzu suna bin kuɗaɗe kuma ayyukan hanyoyin sun tsaya ba a gama ba

Hon Alhassan ya ƙara da cewa "idan ka kalli kuɗaɗen da 'yan kwangila suke bi sun haura naira biliyan 120. Saboda haka idan gayyata ta kai ga tsohon gwamna ba laifi ba ne amma yanzu dai muƙarrabansa muke gayyata domin su mana bayani kan yadda aka ciyo bashi da yadda aka kashe kuɗaɗen."

Ko El-Rufa'i ya mayar da martani?

Har kawo yanzu dai ba a ji ta bakin tsohon gwamnan ba dangane da waɗannan zarge-zargen da ake yi wa gwamnatin tasa.

Sai dai kuma a lokuta da dama ƴaƴan tsohon gwamnan kan yi maganganu ko dai na kai tsaye ko kuma na raragefe wajen kare gwamnatin mahaifin nasu.

Ko a makon nan sai da ɗaya daga cikin ƴaƴan na El-Rufa'i ya wallafa yawan kuɗin da gwamnatin jihar ta Kaduna ta samu na wata-wata daga gwamnatin tarayya.

Ɗan tsohon gwamnan ya ce " jihar Kaduna ta karɓi naira biliyan 18 bayan cire komai da komai. To ta yaya za a ce an kasa biyan ma'aikata albashi?"

Za dai a iya cewa har kawo yanzu ba a ji bakin gwamna mai ci, Malam Uba Sani da na tsohon gwamna Malam Nasiru El-Rufa'i ba. Sai dai masu fashin baƙi na ganin nan gaba kaɗan al'amarin ka iya kai wa ga hakan.

People are also reading