Home Back

"Matawalle Ya Inganta Tsaron Zamfara": APC Ta Fadi Babban Matsalar da Gwamna Ya Jawo

legit.ng 2024/7/2
  • Yayin da ake fama da matsalar tsaro a Zamfara, jam'iyyar APC ta bayyana Gwamna Dauda Lawal a matsayin mai laifi
  • Jam'iyyar ta ce duka abin da ke faruwa laifin Dauda Lawal ne saboda yaki hada kai da Bello Matawalle domin kawo karshen matsalar
  • Sakataren yada labaran APC a jihar, Alhaji Yusuf Gusau shi ya bayyana haka inda ya ba gwamnan shawara kan lamarin

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Zamfara - Jam'iyyar APC a Zamfara ta zargi Gwamna Dauda Lawal kan kara dagula lamarin tsaro a jihar.

Jam'iyyar ta ce gwamnan bai ba da hadin kai ga karamin Ministan tsaro, Bello Matawalle ba domin kawo karshen rashin tsaro a jihar.

APC ta zargi gwamnan Zamfara da rashin hada kai da Matawalle domin dakile rashin tsaro
Jam'iyyar APC ta fadi yadda Bello Matawalle ya inganta tsaron jihar Zamfara. Hoto: Dauda Lawal, Bello Matawalle. Asali: Twitter

Zamfara: APC ta yabawa Matawalle kan tsaro

Sakataren yada labaran jami'yyar a Zamfara, Alhaji Yusuf Gusau shi ya bayyana haka yayin hira da jaridar Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yusuf Gusau ya alakanta hakan da bambancin siyasa da gwamnan ke nunawa ga Matawalle wanda abin takaici ne.

"Mutanen Zamfara na fuskantar matsalolin tsaro saboda Dauda Lawal ya ki hada kai da Matawalle saboda siyasa."
"A bayyane yake tun kafin a zabi Matawalle Minista ya bukaci hadin kai da gwamanti da sauran tsofaffin gwamnoni domin kawo karshen matsalar."
"Amma abin takaici gwamna ga bakin hadiminsa ya yi fatali da kiran inda ya bayyana hakan da cin fuska."

- Alhaji Yusuf Gusau

APC ta ba gwamnan Zamfara shawara

Yusuf ya kirayi Gwamnan Dauda Lawal da ya ajiye siyasa a gefe domin kawo karshen matsalar jihar.

Ya ce tun bayan nadin Matawalle Minista an samu karin jami'an tsaro kan manyan hanyoyi da ke taimakawa matafiya samun sauki.

A cewarsa, kowa ya tabbatar yanzu an samun ingantuwar tsaro fiye da baya saboda yawan jami'an tsaro.

Matawalle ya magantu kan kisan sojoji a Abia

A wani labarin, kun ji cewa karamin Ministan tsaro, Bello Matawalle ya nuna damuwa kan yadda aka hallaka sojoji a jihar Abia.

Matawalle ya sha alwashin zakulo wadanda suka aikata wannan kazamin hari domin tabbatar da fuskantar hukunci.

Asali: Legit.ng

People are also reading