Home Back

BIN DIDDIGI: Shin da akwai luwaɗi, maɗigo da sauyin jinsi a cikin Yarjejeniyar Samoa da Najeriya ta sa hannu?

premiumtimesng.com 2024/8/19
BIN DIDDIGI: Shin da akwai luwaɗi, maɗigo da sauyin jinsi a cikin Yarjejeniyar Samoa da Najeriya ta sa hannu?

Binciken PREMIUM TIMES ya gano cewa akwai batun luwaɗi, maɗigo da sauyin jinsi a daftarin farko na Yarjejeniyar Samoa amma rashin amincewar wasu daga cikin ƙasashe ya tilastawa Tarayyar Turai, EU ta cire sassan daga cikin daftarin.

A ranar Alhamis, Daily Trust ta ruwaito yadda wasu daga cikin ƙungiyoyin addini da na ci gaban al’umma a cikin ƙasar nan ke nuna damuwa game da wasu sassa a cikin yarjejeniyar $150 biliyan ta Samoa wacce gwamnatin Najeriya ta sa hannu a ranar 28 ga Yuni waɗanda suka sharɗanta kare haƙƙin ƴan luwaɗi, maɗigo da sauyin jinsi.

Rahoton jaridar ya dogara ne da ra’ayin da wani lauya mazaunin Lagos, Sonnie Ekwowusi ya rubuta, kuma jaridun BusinessDay, Vanguard da TheCable suka wallafa.

Rahotannin sun jawo masu sharhi sun yi caa kan gwamnatin tarayya inda suke sukarta da yin watsi da mutunci da tabiyyar ƴan Nigeria saboda kwaɗayin bashin ƙasashen waje.

Sai dai, gwamnatin tarayya, a wata sanarwa da ministan yaɗa labarai da wayar da kan al’uma Mohamed Idris ya fitar da yammacin Alhamis, ta ce ba ta sa hannu akan yarjejeniyar ba “sai bayan nazari da tattaunawa tsakanin jami’an ma’aikatar kasafin kuɗi da tsare-tsaren tattalin arziki, ma’aikatar hulɗa da ƙasashen waje da kuma ma’aikatar shari’a.”

Mohammed Idris ya ƙara da cewa gwamnati ta tabbatar “Babu wani daga cikin sassan yarjejeniyar 103 da ya saɓawa Kundin Tsarin Mulkin Ƙasa na 1999 da sauran dokokin Nigeria.”

Gwamnatin Najeriya ta sa hannu a kan yarjejeniyar ne watanni bakwai bayan da aka fara sa hannu akanta a Samoa.
Gwamnatin ta ce ta jinkirta amincewa da ita ne domin samun damar tantance dokar dalla-dalla saboda tabbatar da cewa babu wani sashi da ya saɓawa dokokin Nigeria.

A bara ne dai kakakin Ma’aikatar Hulɗa da Ƙasashen Waje Francisa Omay ta bayyanawa manema labarai cewa “Muna sanar da al’umma Najeriya ba ta cikin ƙasashen da suka sa hannu a Yarjeniyar Samoa ranar Laraba 15 ga Nuwamba 2023 saboda ba ta kai ga amince wa da dokar ba.”

Ta kuma ce “A yanzu haka masu ruwa da tsaki na Nigeria na ci gaba da nazarin yarjejeniyar domin tabbatar da cewa ba ta saɓa wa dokokin ƙasar nan ba.”

PREMIUM TIMES ta ga saƙon da gwamnatin Najeriya ta aikewa EU a lokacin, inda ta ƙalubalanci 13 daga cikin sassan yarjejeniyar.

Daga ciki, gwamnatin Nigeria ta ƙalubalanci Sashi na 9.2, wanda ya shafi Haƙƙin bil’Adama, dimokraɗiyya da aiwatar da doka inda ta ce dama Tsarin Mulkin Najeriya ya na da tanadi game da haƙƙin bil’Adama.

Wannan ya haɗa da “haramcin nuna wariya ta kowacce irin fuska, da ya bai wa Majalisar Dokoki ta Ƙasa damar yin kowacce irin doka da ta kare haƙƙoƙin dukkan rukunin ƴan ƙasa da suka shafi siyasa, tattalin arziki, da ilimi. Wannan ya dace da tanade-tanaden Majalisar Ɗinkin Duniya kan Kare Haƙƙi wadda tuni Nigeria ta sa hannu.”

Wasu sassan da gwamnatin Najeriya ta ƙalubalanta sun haɗa da Sashi na 1 (Manufofi), Sashi na 3 (Tattaunawa kan haɗin kai), Sashi na 4 (Daidaituwar Manufa), da Sashi na 79 (Haɗin kai kan ƙungiyoyin ƙasashen duniya da Majalisu).

Bugu da ƙari, gwamnatin ta ƙalubalanci Sashi na 19 (Manyan laifuffuka da suka shafi ƙasashen duniya); Sashi na 36 (Daidaiton jinsi da kyautata rayuwar mata da ƙananan yara); Sashi na 49 (Cinikayya da cigaba mai ɗorewa); Sashi na 51 (cinikayyar ayyukan fasaha) da Sashi na 97 (Sauran yarjeniyoyi da shirye-shirye)

Akwai kuma Sashi na 101 (Sasanta saɓani da sauke nauyi), Sashi na 22 (Ayyukan fasah), Sashi na 40 (Daidaita jinsi da inganta rayuwar mata), Sashi na 51 (Sauyin yanayi), da Sashi na 3 (Canjin kuɗi).

Tantance zargin

PREMIUM TIMES ta yi nazarin yarjejeniyar mai shafi 172 domin tantance ko akwai batun luwaɗi, maɗigo da sauyin jinsi kamar yadda Daily Trust da sauran jaridu suka wallafa.

Mr Ekwowusi, wanda shi ne ya rubuta maƙalar da jaridun suka dogara da ita wurin wallafa rahotanninsu, ya yi zargin cewa wasu sassan yarjejeniyar sun halatta luwaɗi, maɗigo da sauyin jinsi ta bayan gida.

Lauyan, wanda shi ne shugaban Kwamitin kula da Haƙƙoƙin Bil’Adama da Tsarin Mulki na Ƙuniyar Lauyoyi ta Afirka (AfBA), ya rubuta a maƙalarsa da Daily Trust ta wallafa ranar 3 ga Yuli cewa “Wasu daga cikin sassan yarjejeniyar, musamman ma Sashi na 2.5 da Sashi na 29.5 sun halatta maɗigo da sauyin jinsi, zubar da ciki, keta zarafin matasa, da sauran ɗabi’u da suka saɓawa al’adun ƙasashen Afirka.”

Sai dai wannan fassarar ta Mr Ekwowusi ta saɓa da abinda wakilinmu ya gano a cikin kundin yarjejeniyar da ya nazarta.

Sashe na 2.5 na yarjejeniyar ya ce “Ƙasashen zasu ɗauki matakan kula da yi wa jinsina adalci tare da tabbatar da cewa an yi la’akari da jinsi a duk wasu dokokin gwamnati,” wato bai kawo wata maganar jima’i ba kamar yadda Mr Ekwowusi ya yi iƙirari.

Haka kuma lauyan ya yi kuskure wurin fassara sashi na 29.5 wanda ya ce: “Ƙasashen za su tabbatar da kowa ya samu kayan kula da lafiyar da ta shafi jima’i da haihuwa ciki har da tsarin iyali, ilmintarwa da faɗakarwa, da kuma shigar da lafiyar masu haihuwa cikin tsare-tsare da manufofin ci gaban al’umma.”

Saɓanin da’awar lauyan, wacce jaridun suka yayata babu wani wuri da aka yi batun luwaɗi da maɗigo a wannan sashen.

Daftarin da muka yi nazari da kuma sanarwar da Tarayyar Turai suka fitar sun bayyana cewa Yarjejeniyar Samoa ta mai da hankali ne wurin warware ƙalubalen da suke addabar duniya.

Manfufofinta na son bada gudunmawa ne wurin cimma manufofin ci gaba mai ɗorewa na Majalisar Ɗinkin Duniya da kuma Yarjejeniyar Paris da aka amince da ita ƙarƙashin Yarjejeniyar Majalisar Ɗinkin Duniya kan Sauyin Yanayi.

A ɗaya daga cikin sanarwar da ta fitar, EU ta ce abubuwan da yarjejeniyar ta fi bai wa muhimmanci sun haɗa da kare haƙƙin bil’Adama, dimokraɗiyya da ingantaccen shugabanci, zaman lafiya da tsaro, ci gaban al’umma, bunƙasar tattalin arziki wacce take taɓa kowa, kula da muhalli da sauyin yanayi, da kuma hijirar al’umma.

PREMIUM TIMES ta gano cewa an yi ta sa-toka-sa-katsi daga daftarin farko zuwa samar da kundin ƙarshe na yarjejeniyar – sanarwar gwamnatin tarayya ta bara da wata sanarwa ta Tarayyar Turai sun tabbatar da hakan.

Sanarwar ta EU ta ce yarjejeniyar za ta bunƙasa, kare, da tabbatar da haƙƙoƙin bil’Adama, waɗanda suka shafi zamantakewa, siyasa, tattalin arziki, da al’ada sai dai “wasu daga cikin ƙasashen Afirka, Carribean da Pacific sun ƙi amincewa da batun maɗigo da sauyin jinsi – abinda har cikin ƙasashen EU ba duka ne suka amince da shi ba.”

A sanarwar, EU ta yi batun tanadin Sashi na 36.2 in da ta ce: “an daidaita cewa, ƙasashen za su tabbatar da aiwatar da dukkan yarjeniyoyin ƙasashen duniya da suka riga suka sa musu hannu – musamman Taron Rage Yawan Al’umma, matakan kare haƙƙoƙin jima’i da haihuwa da Matsayar Beijing kan daidaiton jinsi da sauran yarjejeniyoyin da suka biyo baya.”

Sai dai, sanarwar ta ce wannan yarjejeniyar “ba ta cimma manufofin masu tattaunawar EU ba.”

PREMIUM TIMES ta fahimci cewa da fari an sa sassan da suka yi magana kan halatta luwaɗi da maɗigo cikin Yarjejeniyar Samoa, amma rashin amincewar ƙasashen ta tilastawa EU cire waɗannan sassan daga kundin na ƙarshe.

Wannan ya ƙara fitowa fili idan aka yi la’akari da wata sanarwar ta EU, inda ta ce ta na maraba da amincewar da ƙasashen suka yi na bunƙasa haƙƙoƙin bil’Adama ba tare da kowacce irin wariya ba “sai dai ta na takacin cewa Yarjejeniyar ta gaza wurin fitowa ɓaro-ɓaro ta haramta wariya kan bambancin tsarin jima’i da sauyin jinsi.”

EU ta kuma roƙi ƙasashen su “guji nuna bambanci game da tsarin jima’i tare da kawo ƙarshen hukuntawa tare da hukuncin kisa ga mutanen da suke maɗigo da sauyin jinsi…”

Kammalawa

Ta tabbata cewa EU ta amince da luwaɗi, maɗigo da sauyin jinsi kuma ta yi ƙoƙarin jawo ƙasashen dake cikin Yarjejeniyar Samoa su bai wa ƴan luwaɗi, maɗigo da sauyin jinsi kariya. Sai dai ƙin amincewar wasu daga cikin ƙasashen, ciki har da Nigeria ya tilasta mata cire wannan sashin daga cikin kundin da ta wallafa a shafinta ranar 22 ga Disamba 2023.

Lokacin da aka wallafa kundin, Nigeria ba ta kai ga sa hannu kan yarjejeniyar ba, wacce EU ta ce ta fara aiki daga bana kuma za ta ƙare aikinta nan da nan da shekaru 20.

A yanzu haka dai, Sashi na 101 na sabuwar yarjejeniyar ya mayar da hankali ne kan sasanta rikici da sauke nauyi.

Saɓanin abinda aka yaɗa a wasu sassa na kafafen yaɗa labarai, Sashi na 2.2. na sabuwar yarjejeniyar ya bayyana cewa:

“Ƙasashen sun jaddada ƙudirinsu na samar da kyakkyawar alaƙa tsakaninsu ta hanyar girmama alfarmar kowacce ƙasa, da kuma rashin yin amfani da barazana ko ƙarfi wurin keta iyaka ko ƴancin kan wata ƙasa ba, ko kuma kowacce irin hanya da ta saɓawa Kundin Tsarin Mulkin Majalisar Ɗinkin Duniya.”

Najeriya, a matsayinta na ƙasa mai cikakkiyar iko ta sa hannu kan dokar da ta haramta auratayya tsakanin jinsi guda a zamanin Shugaba Goodluck Jonathan.

Wannan ne ya sa masu sharhi ke ganin bai kamata Nigeria ta sa hannu a Yarjejeniyar Samoa ba.

Sai dai masana sun mayarwa da irin waɗannan martani, inda suka ce irin wanann yarjejeniyar ta ƙasashen duniya, ko da an sa mata hannu, dole ne sai an tafka muhawara a Majalisar Dokoki ta Tarayya kamar yadda Sashe na 12(1) na Kundin Tsarin Mulkin Nigeria na 1999 ya tanada.

Rabiu Yusuf, shugaban Kwamitin kula da Yarjejeniyoyin Ƙasashen Duniya na Majalisar Wakilai da Asabe Ndahi, Jami’ar Tsare-tsare ta Cibiyar Kukah, sun bayyana cewa kawo yanzu ba a saka Majalisar Dokoki cikin sabgar Yarjejeniyar Samoa ba.

Mr Yusuf wanda ya yi jawabi a tattaunawar intanet da Cibiyar Kyautata aikin jarida ci gaban al’umma (CJID) ta shirya domin fahimtar matsayin Najeriya game da Yarjejeniyar Samoa ya ce kundin ya bayyana abubuwa da yawa da ƙasar nan za ta amfana da su.

Hukunci

Saɓanin abinda wasu sassa na kafafen yaɗa labarai suka ruwaito, babu wani sashe da ya shafi luwaɗi, maɗigo da sauyin jinsi a cikin Yarjejeniyar Samoa wacce Najeriya ta sa hannu a kai, bisa binciken da PREMIUM TIMES ta yi.

Rahoton Daily Trust bai kawo wani sashe da ya wajabta kare haƙƙin masu luwaɗi, maɗigo da sauyin jinsi ba sai dai ruwaito ra’ayin Mr Ekwowusi, duk da cewa a cikin rahoton sun kawo hirarsu da sakataren gudanarwar NSCIA wande ya ce majalisar ba ta ga wani abu da ya shafi auren jinsi a cikin daftarin yarjejeniyar gwamnatin tarayya ta ba ta, ta duba kafin rattaba hannu.

Haka kuma, fassarar da Mr Ekwowusi, wannan lauyan mazaunin Lagos ya yi a ra’ayin da ya ɓatar da kafafen yaɗa labaran da suka dogara da shi ba daidai ba ce.

People are also reading