Home Back

Ɗaliban Jami’ar Bayero ‘Yan Ajin 2015 Sun Zamanantar Da Ɗakin Karatu Na M.A.Z Sani

leadership.ng 2024/5/18
Ɗaliban Jami’ar Bayero ‘Yan Ajin 2015 Sun Zamanantar Da Ɗakin Karatu Na M.A.Z Sani

Tsofaffin daliban Sashen’ Koyar da Harsunan Nijeriya na Jami’ar Bayero ‘yan shekarar 2015 sun sabunta Dakin Karatu na Sashen tare da gyaran wasu sassa na Sashen a Jami’ar.

A ranar Alhamis 02 ga watan Mayun 2024 aka gudanar da kasaitaccen bikin bude Dakin Karatu na Marigayi Farfesa M.A.Z Sani da tsofaffin daliban Sashen suka sabunta shi bisa jagorancin shugaban daliban na 2015, Alhaji Hassan Baita Ubawaru, wanda ya samu wakilcin Sakataren Kungiyar daliban, Muhammad Bashir Amin.

Sakataren Kungiyar Dalibai 'Yan Ajin 2015, Muhammad Bashir Amin, yayin da yake yi wa Shugaban Jami'ar Bayero bayani yayin bikin bude Dakin Karatu na M.A.Z Sani
Sakataren Kungiyar Dalibai ‘Yan Ajin 2015, Muhammad Bashir Amin, yayin da yake yi wa Shugaban Jami’ar Bayero bayani yayin bikin bude Dakin Karatu na M.A.Z Sani

A nasa jawabin Shugaban Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya na Jami’ar Bayero, Dr. Jibril Shu’aibu Adamu, ya yaba da kokarin daliban ya kuma sanarwa da Shugaban Jami’ar, Farfesa Sagir Adamu Abbas, irin kokarin da daliban suke yi na tallafawa Sashen, inda ya ce ko a kwanan nan tsofaffin daliban sun bai wa Sashen sababbin injinan nadar bayanan takardu uku tare da gyaran wasu sassa na Sashen.

Shugaban Jami'ar Bayero, Farfesa Sagir Adamu Abbas da Dr. Jibril S. Adamu da Alh. Baita Ubawaru yayin bikin bude Dakin Karatu na M.A.Z Sani
Shugaban Jami’ar Bayero, Farfesa Sagir Adamu Abbas da Dr. Jibril S. Adamu da Alh. Baita Ubawaru yayin bikin bude Dakin Karatu na M.A.Z Sani

A nasa jawabin, Shugaban Jami’ar Bayero, Farfesa Sagir Adamu Abbas, ya yaba da kokarin daliban da irin tallafin da suke bai wa Sashen, ya kuma yi alkawarin ci gaba da tallafawa Sashen daga bangaren shugabancin Jami’ar.

Sagir ya ce, Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya shi ne Sashe daya rak da ya fi kowane Sashen hulda da kasashen waje da suka hada da kasar Sin da Holandiya da Jamus da dai sauransu.

A jawabin shugaban daliban, Alh. Hassan Baita Ubawaru, wanda ya samu wakilcin Sakataren kungiyar daliban, Muhammad Bashir Amin, ya ce, za su ci gaba da tallafawa Sashen ta bangarori da dama, tare da aiki kafada-kafada da juna don ganin an inganta harkokin koyo d koyarwa da bunkasa Harshe da Adabi da Al’adun Hausawa.

Alh. Baita Ubawaru yayin da yake jawabi a wurin bikin bude Dakin Karatu na M.A.Z Sani a Jami'ar Bayero.
Alh. Baita Ubawaru yayin da yake jawabi a wurin bikin bude Dakin Karatu na M.A.Z Sani a Jami’ar Bayero.

A nasa jawabin, Alh. Baita Ubawaru, wanda shi ne mahaifin shugaban daliban na 2015, kuma daya daga cikin wandanda suka tallafawa Shugaban Jami’ar wajen kaddamar da bude Dakin Karatun a yayin bikin, ya bayyana farin cikinsa tare da fatan Dakin Karatun ya zama mai amfanar da daliban Sashen da sauran al’umma baki daya.

People are also reading