Home Back

Fasa Kwaurin Fetur: Nijeriya Ta Yi Asarar Biliyoyin Naira – Kwastam

leadership.ng 4 days ago
Fasa Kwaurin Fetur: Nijeriya Ta Yi Asarar Biliyoyin Naira – Kwastam

Shugaban hukumar Kwastam, Bashir Adewale Adeniyi, ya ce Nijeriya ta yi asarar biliyoyin nairori kan annobar fasa kwaurin man fetur.

Adeniyi ya shaida hakan ne a ganawarsa da ‘yan jarida a Yola ta Jihar Adamawa a ranar Litinin.

Ya ce, haramtattun kasuwancin mai da ya janyo rashin daidaiton farashi a tsa-kanin Nijeriya da makwabtanta ya kai intiha.

“Halin da ake ciki ya yi muni matuka. Masu fasa kwauri na amfani da mabam-bantan farashi domin samun riba mai tsoka, tare da dakile kasar daga samun kudaden shiga,” ya shaida.

A cewarsa, domin dakile wannan ta’asar, Kwastam ta kaddamar da rundunar ta musammam mai suna ‘Whirtwing’, inda suka cafke sama da litar man fetur sama da 150,950 da darajar kudinsa ya kai na naira miliyan 105.9 a cikin makwanni bi-yu kacal.

Ya lura kan cewa man da suka cafke na daga cikin irin biliyoyin da Nijeriya ke tafka asara kan masu gudanar da kasuwancin mai ta barauniyar hanya, sai ya yi gargadi da cewa, “Ba su ci gaba da wannan aikin za su dandani kudarsu.

“Muddin ba a tashi tsaye aka dakile wannan mummunar annobar ba, zai kara da-gula mana musayar kudaden kasashen waje, lafta karin kalubale ga tatalin arzi-kinmu da kuma karuwar aikace-aikacen da ba su kan ka’ida.”

Duk da hakan, ya bayar da tabbacin cewa, hukumar ta sha damarar dakile masu gudanar da haramtattun kasuwanci da kuma dawo da martabar man kasar Nijer-iya.

People are also reading