Home Back

‘Ana toshe duk wata kafa da mutanen kirki za su hau mulki a Najeriya’

bbc.com 2024/7/2

‘Ana toshe duk wata kafa da mutanen kirki za su hau mulki a Najeriya’

Mintuna 2 da suka wuce

Yayin da mulkin farar hula ya cika shekara 25 karon farko a tarihin Najeriya, wani ɗan gwagwarmayar mulkin dimokraɗiyya ya bayyana damuwa kan abin da ya kira ‘toshe duk wata kafa da mutanen kirki da masu adalci za su hau mulki’ a ƙasar.

Shehu Sani, wanda yana ɗaya daga cikin ‘yan fafutukar siyasar da suka yi gwagwarmaya a shekarun 1990 don ganin sojoji masu mulki na wancan lokaci sun mayar da ƙasar kan mulkin dimokraɗiyya ya yi zargin cewa shugabannin ƙasar sun yi kaka-gida a kan mulki tare da mayar da siyasa mulkin ɗauki-ɗora.

Ya ce kashe dimokraɗiyya ne a ce jam’iyyu sun koma ƙarƙashin gwamnoni da shugaban ƙasa, sai mutumin da suke so ne kawai zai iya samun takara.

Rashin adalci da rashin gaskiya sai ƙara dawwamar da talauci yake, in ji Shehu Sani.

Ɗan gwagwarmayar wanda ya taɓa zama sanata daga jihar Kaduna, ya kuma zargi mutane da zama masu kwaɗayi da bautawa shugabanni, abubuwan da ya sun taimaka wajen jefa dimokraɗiyya cikin wani hali.

People are also reading