Home Back

NFF Zata Baiwa Supersand Eagles Goyan Baya Daidai da Sauran Tawagogi- Musa Gusau

premiumtimesng.com 2024/7/5
NFF Zata Baiwa Supersand Eagles Goyan Baya Daidai da Sauran Tawagogi- Musa Gusau

Daga Muhammad Suleiman Yobe

Hukumar kwallon kafa ta Najeriya (NFF) ta bayar da tabbacin cewa zata baiwa tawagar ƙwallon yashi ta ƙasa Supersand Eagles dukkanin kulawa dake take buƙata kamar sauran tawagogin kasar.

Shugaban hukumar kwallon ƙafa ta Najeriya, Ibrahim Musa Gusau ne ya bayar da wannan tabbacin a lokacin kaddamar da kananan kwamitocin wasannin Futsal da na kwallon kwando a sakatariyar hukumar NFF da ke Abuja.

Ya ce hukumar ta himmatu wajen ganin tawagar kwallon yashi, wadda aka fi sani da Supersand Eagles, ta samu kulawa irin ta sauran tawagogin kasa, idan aka dawo da su gasar ƙasa da ƙasa.

“Najeriya babbar kasa ce ta kwallon yashi, kuma ba zai dace ba idan muka ci gaba da kaurace wa wasu wasannin da wasu kungiyoyin kasashen Afirka ke takawa ba-inji Gusau

Ya ƙara da cewa “Za mu yi duk abin da ya dace don dawo da Najeriya fagen kwallon yashi.

“Ina tabbatar wa kwamitin nan cewa zan bawa kwallon yashi da futsal dukkanin gudummawar da suke buƙata kamar sauran tawagogi.

Idan dai za a iya tunawa dai ‘yan wasan Supersand Eagles sun sha lashe kofuna da kyautuna a lokuta daban-daban a baya, inda suka lashe gasar cin kofin kwallon yashi na nahiyar Afirka a shekarar 2007 da 2009.

Tawagar ta kuma sha wakiltar Afirka a gasar cin kofin kwallon yashi na duniya a lokuta da dama, ciki har da kai wasan daf da kusa da na karshe a birnin Ravenna na Italiya a shekarar 2011 kafin ta sha kashi a hannun Brazil a ƙarin lokaci.

Hukumar NFF ta yanke shawarar janye kungiyar daga gasar kasa da kasa shekaru biyar da suka gabata, bayan ƙasa yin kokari a wasan ƙwallon yashi na duniya da aka buga a ƙasar Paraguay.

Mamba a kwamitin zartarwa na NFF, Otuekong Nse Essien shi ne zai kasance shugaban kwamitin, tare da Alhaji Ahmed Yusuf (Fresh) a matsayin mataimakin shugaba.

Sauran membobin sun haɗa da Hon. Suleiman Yahaya-Kwande, tsohon mamban kwamitin zartarwa na NFF kuma shugaban FA na jihar Filato, Richard Jideaka, babban dan jarida; Aminu Mohammed Inuwa, Liamed Gafaar, Shugaban Hukumar FA ta Jihar Legas da dai sauransu.

People are also reading