Home Back

'Ba jami'in gwamnatina da zai sayi kadarar gwamnati idan na zama shugaban Ghana'

bbc.com 2024/8/22

Asalin hoton, Getty Images

John Dramani Mahama
Bayanan hoto, John Dramani Mahama

Dan takarar babbar jam'iyyar hamayya a Ghana, kuma tsohon shugaban kasar John Dramani Mahama, ya lashi takobin daukan tsattsauran mataki kan matsalar cin hanci da rashawa idan ya yi nasara a zaben shugaban kasar da za a yi a watan Disamba mai zuwa.

A wani taron manema labarai a birnin Accra, Mr Mahama, ya yi alkawarin kwato dukkan kadarorin gwamnati da aka sace da hukunta jami'an da aka samu da cin hanci da rashawa a wannan gwamnati.

‘Zan sanya ido kan wadanda na nada mukamai, ina tabbatar wa al'ummar Ghana zan dauki matakin ba sani ba sabo don hukunta jami'an da aka samu da rashawa da masu taimaka musu a cikin wannan gwamnatin,'' in ji tsohon shugaban kasar ta Ghana.

A watan Disambar shekarar nan ake sa ran 'yan Ghana za su fita rumfunan zaben shugaban kasa da 'yan majalisu.

Kasar na fama da matsaloli da dama, babba daga ciki ita ce ta cin hanci da rashawa.

Kuma ita ce ta fi ci wa 'yan kasar tuwo a kwarya, inda ake yawan tattaunawa a kai.

Mr Mahama, ya jaddada cewa babu wani daga cikin masu mukaman gwamnati da za a bari ya sayi kadarorin gwamnati.

A shekarar 2018 ne shugaban Ghana na yanzu Nana Akufo Addo, ya samar da ofishin mai shigar da kara na musamman na gwamnati, da nufin hukunta jami'an gwamnati da aka samu da cin hanci da rashawa, sai dai har yanzu ba ta sauya zani ba.

Sai dai ma matsaloli da dama da suka yi ta tasowa hukumar, ciki har da murabus din shugabanta Martin Amadu wanda ya zargi Shugaba Nana Akufo-Addo, da tsoma baki a ayyukansu, zargin da ya musanta.

John Dramani Mahama, ya kuma sha alwashin farfado da tattalin arzikin kasar, da samar da ayyukan yi ga matasa.

A watan Disambar shekarar nan ne za a gudanar da zaben shugaban kasar Ghana, inda 'yan takara da dama za su fafata ciki har da mataimakin shugaban kasa na yanzu Mahamudu Buwamia.

People are also reading