Yadda Hukumar EFCC Ta Samu Nasarar Kwato N120bn a Cikin Watanni 6
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Shugaban hukumar yaƙi da yi wa tattalin arziƙin ƙasa zagon ƙasa (EFCC), Ola Olukoyede, ya yi magana kan nasarorin da hukumar ta samu tun bayan da ya fara jagorantarta.
Olukoyede a ranar Talata ya bayyana cewa hukumar ta ƙwato Naira biliyan 120 daga hannun ƴan damfara a Najeriya cikin watanni shida da hawansa mulki.
Ya bayyana hakan ne a Abuja a wani taron manema labarai a hedikwatar hukumar ta EFCC, rahoton jaridar PM News ya tabbatar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Olukoyede ya jaddada cewa Najeriya na bukatar EFCC domin tsira yayin da hukumar ke ci gaba da ƙwato kuɗaɗen sata daga hannun mutane kusan kullum.
"Muna buƙatar EFCC, muna buƙatar wannan hukuma domin mu tsira, mun share hawayen mutane da dama da aka cuta, mutane masu ɗumbin yawa da aka zalunta, kullum muna ci gaba da ƙwato kuɗaɗe a hannun mutane."
"A cikin watanni shida da na yi, mun ƙwato sama da Naira biliyan 120 kuma mun sanya an yanke hukunci sama da 1,600."
- Ola Olukoyede
Shugaban na hukumar EFCC ya kuma zargi tsohon gwamnan jihar Kogi da cire kuɗi daga asusun gwamnatin jihar Kogi domin biyan kuɗin makarantar yaransa.
Olukoyede ya zargin Yahaya Bello da cirar Dala dubu 720 domin biyan kuɗin makarantar ƴaƴansa, inda ya sha alwashin cewa zai ajiye aiki idan bai kammala binciken tsohon gwamnan ba, cewar rahoton tashar Channels tv.
A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar EFCC ta sake shigar da sabuwar ƙara kan tsohon gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele.
A cikin ƙarar da hukumar yaƙi da cin hancin ta shigar, ta zargi Emefiele ta zargi amfani da sanya hannu kan buga N684m a kan kuɗi har N18.9bn.
Asali: Legit.ng