Home Back

An bude rumfunan zabe a Afirka ta Kudu.

dw.com 2024/7/5
Wahlen in Südafrika 2024
Hoto: Nic Bothma/REUTERS

Hukumar zaben kasar ta ce masu kada kuri'a miliyan 27 ne aka yi wa rajista, kuma tuni fiye da miliyan daya da rabi da suka yi rajista don kada kuri'a da wuri suka fara a kwanaki biyu na kafin zaben wato ranakun Litinin da Talata. 

Jam'iyyar ANC mai mulki a kasar da ta lashe manyan zabukan a karo shidda, yanzu haka tagomashinta na dusashewa , inda aka ce akwai yiwuwar ta rasa rinjaye duba da cewar tana da kasa da kaso 50 cikin dari na magoya bayanta.

Afirka ta Kudu da ke da al'umma miliyan 62 kuma kasa da ke da karfin tattalin arzikin masana'antu, na fama da tarin kalubale da suka hada da cin hanci da rashawa da rashin aikin yi a tsakanin al'umma kuma rabin al'ummar kasar na rayuwa ne a cikin talauci.
 

People are also reading