Home Back

Fetur Ya Yi Tsada: Dillalan Mai Sun Tsunduma Yajin Aiki, an Rufe Gidajen Mai 2,000

legit.ng 2024/7/2
  • Rahotanni da muka tattara na nuni da cewa dillalan man fetur karkashin kungiyar IPMAN sun shiga yajin aiki a Arewa maso Gabas
  • An ruwaito cewa hukumar Kwastam ce ta kwace wasu motocin dakon mai na IPMAN bisa zargin suna safarar fetur zuwa Kamaru
  • Shugaban IPMAN na shiyyar, Dahiru Buba, ya ce sun rufe gidajen mai 2,000, yayin da farashin lita a yanzu ya haura zuwa N1,500 a jihohin

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Yola, jihar Adamawa - Kungiyar dillan mai ta kasa (IPMAN) ta ce ta dakatar da dukkanin jigilar man fetur zuwa gidajen mai a fadin jihohin Adamawa da Taraba.

Haka zalika IPMAN ta garkame akalla gidajen mai 2,000 da ke mallakin mambobinta a shiyyar ta Arewa maso Gabashin ƙasar.

IPMdddd
IPMAN ta tsunduma yajin aiki, an rufe gidajen mai 2,000 Asali: Getty Images

Kamar yadda jaridar Tribune ta ruwaito, IPMAN, ta rufe gidajen man ne kasa da awanni 48 bayan ta yi zargin jami'an hukumar Kwastam sun ƙwace tankokin man mambobinta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwastam ta ƙwace motocin man IPMAN

Shugaban ƙungiyar IPMAN reshen Adamawa da Taraba, Dahiru Buba ya ce Kwastam ta kwace motocin dakon man su saboda zargin suna safarar fetur zuwa Kamaru.

Masu bumburutun man fetur a Kamaru, Benin da Togo sun shafe shekaru suna dogaro da man fetur da ake shigar masu daga Najeriya, in ji rahoton Reuters.

A karkashin atisayen "Whirlwind", jami'an Kwastam sun kama motocin dakon man IPMAN amma suka sake su bayan 'yan kungiyar sun yi zanga-zanga.

IPMAN ta rufe gidajen mai sama da 1,800

Sai dai Dahiru Buba ya ce Kwastam ta sake kama wasu ƙarin motocin man tare da rufe wasu gidan mai, abin da ya tilasta IPMAN rufe gaba daya gidajen man yankin.

IPMAN ta bayyana cewa:

"Mun rubutawa hukumar Kwastam wasika kan wannan lamari amma babu amsa daga wajensu, wannan ne ya tilasta mu shiga yajin aiki.
"Mun rufe sama da gidajen mai 1,800. Wannan ce kasuwancin mu, ba za mu zura idanu mu kyale hukuma tana cin kashi ga 'yan kungiyarmu ba."

Farashin litar fetur ya lula zuwa N1500

A halin yanzu dai an ruwaito cewa masu bumburutun fetur a jihohin Adamawa da Taraba sun fara cin karensu ba babbaka, inda suka tsugaga kudin fetur din.

Wani ma'abocin shafin X, Habu Sadeik, ya wallafa a shafinsa na @HabuSadeik cewa litar fetur ta haura zuwa N1,500 daga jiya Litinin.

Sahara Reporters ta ce ba iya gidajen mai mallakin IPMAN kadai aka rufe ba, hatta gidajen mai mallakin kamfanin NNPC suna a garkame a wadannan garuruwan.

Kano ta yi sabon kwamishinan'yan sanda

A wani labarin, mun ruwaito cewa, sabon kwamishinan'yan sanda da aka tura zuwa Kano, Salman Dogo Garba ya kama aiki gadan-gadan.

Wannan na zuwa ne bayan da CP Usaini Gumel ya samu karin matsayi zuwa mataimakin Sufeta Janar na 'yan sanda, kuma ya mika mulki ga CP Salman a ranar Litinin.

Asali: Legit.ng

People are also reading