Fetur Ya Yi Tsada: Dillalan Mai Sun Tsunduma Yajin Aiki, an Rufe Gidajen Mai 2,000
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Yola, jihar Adamawa - Kungiyar dillan mai ta kasa (IPMAN) ta ce ta dakatar da dukkanin jigilar man fetur zuwa gidajen mai a fadin jihohin Adamawa da Taraba.
Haka zalika IPMAN ta garkame akalla gidajen mai 2,000 da ke mallakin mambobinta a shiyyar ta Arewa maso Gabashin ƙasar.
Kamar yadda jaridar Tribune ta ruwaito, IPMAN, ta rufe gidajen man ne kasa da awanni 48 bayan ta yi zargin jami'an hukumar Kwastam sun ƙwace tankokin man mambobinta.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban ƙungiyar IPMAN reshen Adamawa da Taraba, Dahiru Buba ya ce Kwastam ta kwace motocin dakon man su saboda zargin suna safarar fetur zuwa Kamaru.
Masu bumburutun man fetur a Kamaru, Benin da Togo sun shafe shekaru suna dogaro da man fetur da ake shigar masu daga Najeriya, in ji rahoton Reuters.
A karkashin atisayen "Whirlwind", jami'an Kwastam sun kama motocin dakon man IPMAN amma suka sake su bayan 'yan kungiyar sun yi zanga-zanga.
Sai dai Dahiru Buba ya ce Kwastam ta sake kama wasu ƙarin motocin man tare da rufe wasu gidan mai, abin da ya tilasta IPMAN rufe gaba daya gidajen man yankin.
IPMAN ta bayyana cewa:
"Mun rubutawa hukumar Kwastam wasika kan wannan lamari amma babu amsa daga wajensu, wannan ne ya tilasta mu shiga yajin aiki.
"Mun rufe sama da gidajen mai 1,800. Wannan ce kasuwancin mu, ba za mu zura idanu mu kyale hukuma tana cin kashi ga 'yan kungiyarmu ba."
A halin yanzu dai an ruwaito cewa masu bumburutun fetur a jihohin Adamawa da Taraba sun fara cin karensu ba babbaka, inda suka tsugaga kudin fetur din.
Wani ma'abocin shafin X, Habu Sadeik, ya wallafa a shafinsa na @HabuSadeik cewa litar fetur ta haura zuwa N1,500 daga jiya Litinin.
Sahara Reporters ta ce ba iya gidajen mai mallakin IPMAN kadai aka rufe ba, hatta gidajen mai mallakin kamfanin NNPC suna a garkame a wadannan garuruwan.
A wani labarin, mun ruwaito cewa, sabon kwamishinan'yan sanda da aka tura zuwa Kano, Salman Dogo Garba ya kama aiki gadan-gadan.
Wannan na zuwa ne bayan da CP Usaini Gumel ya samu karin matsayi zuwa mataimakin Sufeta Janar na 'yan sanda, kuma ya mika mulki ga CP Salman a ranar Litinin.
Asali: Legit.ng