Home Back

Basarake Ya Sha Kunya Bayan NDLEA Ta Kama Shi da Kayan Maye, Ta Cafke Wani a Kano

legit.ng 2024/10/5
  • Yayin da take ci gaba da yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi, hukumar NDLEA ta cafke mutane da dama
  • Hukumar ta kama wani basarake a jihar Osun mai suna Ba'ale Ige Babatunde da wani mai bautar kasa a Kano
  • Hakan ya biyo bayan wani samame da ta kai a jihar Lagos inda ta yi nasarar cafke gungun masu safarar kwayoyi

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Hukumar yaki da hana fataucin kwayoyi ta NDLEA ta yi gagarumar nasara kan masu ta'ammali da kwaya.

Hukumar ta yi nasarar cafke wasu mutane ciki har da wani basarake a jihar Osun inda aka same shi da muggan kwayoyi.

NDLEA ta cafke mai bautar kasa a Kano da wani basarake
Hukumar NDLEA ta yi nasarar cafke wasu da miyagun kwayoyi a Kano da Osun. Hoto: @ndlea_nigeria. Asali: Twitter

Nasarar da NDLEA ta samu a Osun

Kakakin hukumar, Femi Babafemi shi ya tabbatar da haka a cikin wata sanarwa da aka wallafa a shafin X a yau Lahadi 7 ga watan Yulin 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

NDLEA ta kama muggan kwayoyin ne a hannun basaraken yankin Akarabata da ke karamar hukumar Ile-Ife da ke jihar.

Hukumar ta cafke wanda ake zargin mai suna Ba'ale Ige Babatunde a ranar Juma'a 5 ga watan Yulin 2024.

Wanda ake zargin mai shekaru 50 an same shi da tulin ganyen tabar wiwi da nauyinsa ya kai kilo biyar.

Kano: NDLEA ta kama mai bautar kasa

A wani farmakin da hukumar ta kai a jihar Kano, an samu wani matashi mai bautar kasa mai shekaru 25 da kayan shaye-shaye.

Wanda ake zargin mai suna Yusuf Abdulrahman yana zaune ne a gidajen masu bautar kasa da ke Sumaila a jihar.

Har ila yau, hukumar ta kai samame jihar Lagos tare da kama wasu mutane guda uku da muggan kayan shaye-shaye.

Wadanda aka kaman sun hada da Agabkoba John da Ijeoma Chinwe da Okoye Ifeoma da ke fitar da shi ketare.

NDLEA ta magantu kan gwaji kafin aure

Kun ji cewa Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA) ta shawarci ma'aurata domin kare ta'ammali da kwayoyi tsakaninsu.

Shugaban NDLEA a Kano, Abubakar Idris Ahmad ya bayar da shawarar cewa a rika tabbatar da yin gwajin duba amfani da kwayoyi gabanin aure.

Asali: Legit.ng

People are also reading