Gwamnatin Tarayya za ta fara gagarimin aikin haƙo ɗanyen man fetur a Jihar Ogun – Lokpobiri
Gwamnatin Tarayya za ta fara gagarimin aikin haƙar ɗanyen man fetur a Jihar Ogun, kamar yadda Ƙaramin Ministan Fetur, Lokpobiri ya tabbatar.
Ya ce hakan ya zo ne daidai lokacin da gwamnatin tarayya ke buƙatar ƙarin kuɗaɗen shiga a ɓangaren ɗanyen mai da gas.
Lokpobiri ya ce za a fara aikin haƙar a wasu wurare a faɗin Jihar Ogun, saboda Jihar ko tantama babu akwai ɗanyen mai a cikin ta.
Ƙaramin Ministan Fetur, Heineken Lokpobiri, ya bayyana haka a ranar Juma’a, yayin da ya kai ziyara Ofishin Gwamnan Jihar Ogun, a Abeokuta, babban birnin Jihar.
Lokpobiri ya kai ziyarar tare da manyan masu hannu a harkokin man fetur da gas daban-daban, cikin su har da Shugaban NNPCL, Mele Kyari.
Ya ce Jihar Ogun na ɗaya daga ɓangaren Dahomey Basin, wurin da ake da kyakkyawan zaton akwai ɗanyen mai kwance maƙil a ƙasa.
Ya ce sun kai ziyara Jihar Ogun ne domin su nuna irin gaggawar fara aikin wanda Gwamnatin Tarayya ke so a yi, domin ƙara samun hanyoyin kuɗaɗen shiga ta hanyar ɗanyen mai.
Ya ce ɗanyen mai ne hanya mafi saurin kawo wa Najeriya kuɗaɗen shiga masu tarin yawa.
A zamanin mulkin Buhari an ƙaddamar da aikin haƙar ɗanyen mai a yankin Kolmani da ke tsakanin jihohin Bauchi da Gombe.
Sai dai kuma tun bayan ƙaddamar da aikin, har yau shiru ka ke ji babu labari kuma babu ƙarin bayani.