Home Back

Matsayar Ƙungiyar Sarakunan Arewa Kan Rikicin Sarki Biyu A Kano

leadership.ng 2024/7/1
Matsayar Ƙungiyar Sarakunan Arewa Kan Rikicin Sarki Biyu A Kano

Majalisar Sarakunan Gargajiya ta Arewa Ƙarƙashin Jagorancin Mai Alfarma Sarkin Musulmi, ta lura da halin da Kano ke ciki domin ya shafi martabarmu sarauta a ƙasar Hausa.

Cikin wata sanarwa a rubuce da jaridar Daily Trust ta wallafa, majalisar ta yi kira ga dukkanin ɓangarorin biyu da su tabbatar da gudanuwar zaman lafiya da kwanciyar hankali, kuma rahotanni sun bayyana cewa guda daga ciki ya garzaya kotu don haka yanzu magana na ƙarƙashin shari’a.

Sanarwar na ɗauke da sa hannun shugaban kwamitin gudanarwa mai martaba Lawal Hassan Gummi OFR, Sarkin Gummi. Shugaban Kwamitin Gudanarwa na majalisar Sarakunan Gargajiya ta Arewa (NTRC).

Majalisar ta yi addu’ar Allah ya ƙaro zaman lafiya a Kano da ma Najeriya baki ɗaya.

Kano

People are also reading