Tirela Ta Sake Kashe Bayin Allah a Kano, Babbar Motar da Ta Dauko Mutane 90 Tayi Hadari
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano- Mutanen dake kusa da Dangwaro flyover a kusa da titin Kano-Zaria sun shiga tashin hankali bayan hadarin babbar mota ya kashe mutane akalla 25.
Babbar mota mai dauke da mutane kimanin 90 ce ta yi hadari saboda abin da hukumar kare afkuwar hadurra ta kasa (FRSC) ta kira da gudun ganganci.
Jaridar Vanguard ta wallafa cewa tirelar ta auno a guje ne sai motar ta kwacewa direba, lamarin da ya jawo wasu 25 suka rasa rayukansu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mutane da dama sun jikkata a hadarin da ya afku ranar Litinin a jihar Kano, inda mutane 53 suka samu mabambantan raunuka, kamar yadda Daily Post ta wallafa.
Jami'in hulda da jama'a na hukumar, Abdullahi Labaran ya tabbatarwa Legit afkuwar hadarin da ya ce an samu ceto wasu mutum 12 babu ko kwarzane.
Hukumar kare afkuwar hadurra ta kasa, reshen jihar Kano ta gargadi matuka manyan ababen hawa su guji gudun wuce sa'a.
Shugaban hukumar a jihar, Ibrahim Abdullahi ya kuma ja kunnen masu loda dabbobi, kaya da motoci yayin tafiye-tafiye.
Ya ce irin wannan na jawo munanan hadurra dake kawo asarar rayuka, yayin da wasu za su iya samun mugayen raunuka.
A baya mun kawo labarin yadda wata babbar mota ta kutsa cikin masallata a jihar Kano tare da kashe mutane 14 nan take.
Masallatan dake sallar Juma'a a garin Imawa da ke karamar hukumar Kura na tsaka da sallah lokacin da motar ta kwace ta shiga cikinsu.
Asali: Legit.ng