Home Back

Kasashen duniya za su tallafa wa gina Sudan

dw.com 2024/5/18
Frankreich I Internationale humanitäre Konferenz für Sudan und Nachbarländer
Hoto: Thomas Koehler/IMAGO

Kasashen duniya sun yi alkawarin samar da tallafin biliyan biyu na Yuro domin sake gina Sudan tare da yin kashedi ga masu ruwa da tsaki wajen tallafa wa bangarorin manyan hafsoshin sojin kasar da ke yaki a tsakaninsu.

Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya bayyana cewa da akwai yiwuwar an aikata laifukan yaki da kisan gillar bil'Adama a Sudan, lamarin da ya ce ba abun ba ne da za a yi gum da baki ana kallo ba.

Daga nasa bangare kwamishinan kare hakkin dan Adam na Majalisar Dinkin Duniya Volker Türk, garkadi ya yi a game da rikidewar yakin zuwa rikicin kabilanci makamancin wanda kasar ta Sudan da ke Gabashin Afrika ta yi fi fama da shi a shekarun baya.

A daya gefe kuma ma'aikatar harkokin wajen Djibuti ta mika tayi ga Majalisar Dinkin Duniya na ta bude hanyoyin shigar da kayan agaji ga al'ummar Sudan daga kasar.

MInistan harkokin wajen Djibuti Mahmoud Ali Youssouf ya ce idan har kawo wannan lokaci batun tsagaita wuta ya ci tura a Sudan to ya zama wajibi a samar da hanyar kai dauki ga miliyoyin al'umma da wannan tashin hankali ya jefa cikin halin la'illaha'ula'i.

Kazalika Mahmoud Ali Youssouf ya kara da cewa al'ummar Sudan na fama da matsalar karancin ruwan sha da abinci da magunguna lamarin da ka iya haddasa barkewar cututuka.

Jami'in diflomasiyyan ya kuma ce Djibuti da ke jagorantar shugabancin kungiyar kasashen IGAD da Tarayyar Afrika na a shirye domin shiga tsakani don warware rikicin na Sudan, sannan kuma ya karfafa gwiwa ga matakin komawa kan teburin tattanawa da Saudiyya da Amurka ke jagoranta a birnin Riyadh kan wannan yaki da cika shekara guda da barkewa a ranar 15.04.2024. 

People are also reading