Home Back

Wata Hajiya ta faɗo daga saman bene a Madina ya yin da wani Alhaji ya yi rasuwar farad-daya, dukansu daga jihar Kwara

premiumtimesng.com 2024/7/5
Pilgrims
Pilgrims

Hukumar Alhazai ta jihar Kwara na mika sakon ta’aziyya ga iyalan mahajjatannta biyu da suka rasu a birnin Madina na kasar Saudiyya.

Saliu Mohammed, wanda ya zo a rukunin Batch 3 na tawagar jihar, ya rasu ne a sashin kula da marasa lafiya na wani asibitin gwamnati da ke Madina bayan ya yi fama da gajeruwar rashin lafiya.

Ita kuwa Hajiya Hawawu Mohammed ta rasu ne biyo bayan wani bincike da hukumomin Saudiyya suka yi, inda suka gano cewa ta faɗo ne daga saman benen Otel ɗin da ta ke a Madina.

A dalilin haka ne hukumar Alhazai ta jihar ta yi jimamin abinda ya faru sannan kuma da mika ta’aziyyarta ga ƴan uwan mamatan.

People are also reading