Home Back

Man United za ta kori ma'aikata 250

bbc.com 2 days ago
Old Trafford

Asalin hoton, Getty Images

Manchester United za ta rage ma'aikata 250 a wani tsarin rage kashe kuɗi da soke wasu abubuwa marasa mahimmci.

Daraktan United, Sir Dave Brailsford shi ne ya ja ragamar bitar yadda ma'aikata ke gudanar da aiki a ƙungiyar bayan da aka mai kamfanin Inoes ya mallaki kaso mafi tsoka a hannun jari a cikin Disamba

Tun farko Sir Jim Ratcliff ya sanar da ma'aikanta tsarin da yake da shi na cewar zai ci gaba da aiki tare da su.

To sai dai wasu rahotanni daga ƙungiyar ya ce United tana bukatar rage kashe kudi, da kuma rage wasu ɗawainiyar gudanarwa.

A bitar da ƙungiyar ta yi ya ce girman ma'aikata da yawansu baya shafar ƙwazon United, wadda take da masu mata aiki fiye da wadanda take bukata.

Kawo yanzu United ba ta fayyace aikace-aikacen ba, amma tana da ma'aikata da ƴan wasa 1,150.

Tuni kuma babban jami'in ƙungiyar na riƙon ƙwarya, Jean-Claude Blanc ya sanar da wannan shirin a wani taro da ya yi a gaban mutum 800.

Wasu na ganin hakan zai kawo koma baya a kakar da United za ta fara ta 2024/25 da cewar rashin sayen ƴan wasan da ya dace, shi ne ya kawo asarar da United ke yi, inda hakan ya shafi a rage ma'aikata.

Rabon da United ta lashe Premier League tun 2012/13. Ta kuma kashe £1.5bn wajen sayen ƴan wasa, wadanda wasu daga cikinsu ba su da daraja a kasuwar tamaula.

United ta taya mai tsaron bayan Everton, Jarrad Branthwaite kan £35m amma ba a sallama mata ba, wadda ke fatan sayen mai tsare baya guda biyu da ɗan kwallon gaba daya.

Haka kuma United ta ware £50m wajen bunkasa filin atisayenta da ke Carrington, wanda mata masu buga tamaula a ƙungiyar suke amfani da shi a baya, yanzu sun samu filin da za suke buga wasanninsu.

Tuni an tsara yadda za a rage ma'aikanta da wadanda hakan zai shafa.

People are also reading